Umm Adiyya

Hannunshi yake kadawa kan sitiyarin motar, yana tafe yana tunanin abubuwa da dama, kwarai ya san cewa ba karamin kuskure yayi ba da ya sake barin Umm Adiyya ta shiga rayuwarsa ko da kuwa ta fuskar aiki ne, duk da kasancewar ba yanda za ayi ya yakice ta daga rayuwarsa saboda abun da ya hadasu ba karamin abu bane da zai warware a dare daya, abun da ya hadasu dangataka ce da ba ta rabewa ba, a tunaninshi ya mance da ita ya sa ta a gefe bazata taba tayar masa da abubuwan da ya zaci ya adanasu ya boyesu a wani lungu a can cikin kirjinsa ba, sai dai yau abun da ya gani a tare da Adiyya sun motsa masa abubuwa da dama masu dadi da masu daci.

Amma ya zama dole ya dubi bangaren dacin yayi aiki da shi saboda hakan zai fi fishe su, daga shi har ita. Har rana mai kaman ta yau bazai taba mance abunda ya faru ba. Birki yaja da karfi a dalilin wata motar da suka kusa yin karo, ashe tsabar tunani ya bar kan hanyarsa ya hau wata daban.

“Zaid Abdurrahman ka wuce haka!” Ya fada a bayyane yayinda ya yanki kwanar Darussalam Close dake Wuse 2 inda shiryayyen gidansa yake.

2 thoughts on “Umm Adiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *