Umm-Adiyya Tsakure

Ya fi sau goma tana ƙarewa takardun da ke gabanta kallo, saboda ta gano inda ta yi kuskure, amma sam! Ta gaza samo wuri koda ɗaya ne, ita kanta ta san ta ƙona lokacinta wajen tsara wannan rahoton, domin ta bi komai daki-daki cikin tsari, sannan ta yi rubutun.

Agogonta ta kalla, domin kuwa lokacin da ya ɗibar mata ya cika, ga shi an kusa tashi, saboda haka dole ta san abin faɗa masa. Kodayake ta riga ta san ɓata lokacinta ma take yi, domin kuwa tunda ya rantse, sai ya ga kasawarta a duk abinda ta yi, ba abinda za tayi masa ta burge.

Wannan ya sa ta hada kan takardun ta jera su, sannan ta shigar da abin da ya kamata ta shigar a na’ura mai ƙwaƙwalwa cikin shafin kamfanin. “Ai idan ka san wata, ba ka san wata ba.” Ta furta ƙasa-ƙasa gudun kar su Oga Akim su ji ta. Kasancewar su uku suka rage a cikin ofishin nasu, sauran ma’aikata ukun yau sun fita aikin fili, (Field work).

Jakarta ta ɗaga ta kimtsa komanta a ciki, cikin shirin tafiya gida saboda ta kula lokacin tashi ya gabato, sai a lokacin ta mulke hannunta man kariya daga ƙwayoyin cuta, (Sanitizer) da ke cikin Jakarta, wanda kaɗan daga cikin ɗabi’un Oga Musa da ta ɗauka kenan a iya fara aikinta da su watanni uku da suka gabata.

Umm Aɗiyya Zubair, Umm A. Kamar yadda kowa yake kiranta ko kuwa Ummu ga ‘Yan gargajiya ko manyan cikin dangi. Ta miƙa duka aikinta na ranar ga shugabanta wanda yake duba ayyukanta kafin a miƙa su ga Oga kwata-kwata. Sai dai yau a maimakon ya yi mata fara’a haɗe da sai da safe. Alama ya yi mata da ta zauna, bari ya duba, idan ba matsala, sai ta wuce.

Shiru ta yi tana kallon mutumin da tsakar kansa yake sheƙi, tsabar yadda yake tal! Ba ko burbuɗin gashi, ga wasu gilasai rau a idanunsa masu ƙarin ƙarfin idanu. A ganin farko, ba za ka ce Oga Akimu yare bane, saboda yadda kullum za ka gan shi cikin shiga na hausawa, sannan fuskarsa tamkar wani bafulatani, sai ya buɗi baki zai yi magana, za ka fahimci tsantsar bayarabe ne, na ƙarshe, don ko turanci yake yi za ka fahimci haka.

Bayan shi kuwa teburin Jamila ce a gefensa, wacce a halin yanzu ba ta nan sun fita tare da Oga Musa, wanda yake kusan matsayinsu ɗaya da Oga Akimu a ofishin. Ba laifi, daga fara aikinta tare da su, sun saba ƙwarai, idan ka ɗebe rashin sukuni da take samu daga wurin mugun murɗaɗɗen shugaban kamfanin, ko ma menene dalilinsa na ba ta aikin, tunda ya tsaneta, har haka oho?

Ita ma maganinta kenan, da har ta miƙa takardar neman aikin a nan. (Application), da ace ta fahimci asalin shi mai kamfanin da tuni ta tsere, tunda kaf garin ba shi bane mutum na ƙarshe da za ta iya aiki da ma’aikatansa.

Koda yake ita ta ɗorawa kanta wannan masifar, da ta nace ita sai NGO ko kuma kamfani mai zaman kansa za ta yi aiki. Idan banda haka, ayyuka nawa ta tsallake ta yiwo nan, da har za a zazzare mata idanu ana sha mata ƙamshi?

Hannu ta sa ta karɓi takardar da Oga Akim ke miƙa mata, “Ga wannan mabuɗin, shiga shafinmu na yanar gizonki, ya samu (Password), wanda aka fitar bayan gyagije shafin kamfani.

Ga naki nan da aka buɗe miki, saboda haka ko daga gida za ki iya ƙarasa wasu ayyukan.” Ya faɗa cikin turancinsa mai cike da harshen yarabanci.

Murmushi ta ƙago masa, ta yi godiya haɗe da saɓa jakarta ta yiwa Ayo (Ayodele) ban-kwana, wanda bai cika magana ba, duk ofis ɗin, sai ku wuni bai ce maku komai ba, dama da shi da Oga Musa ne, shiru-shiru, ɗan surutu kam sai Hasan, ita ma Ummu A. ɗin haka ta fi so, don sam ita ba ta ra’ayin ta zage tana ta shewa tana surutu da ma’aikatan ofis ɗinsu.

Sai da ta faki ƙayataccen babban falon da ya haɗa ƙofofin ofis-ofis na kamfanin, ta tabbatar ba za ta haɗu da damuwa ba, sannan ta danna kai, cikin ɗan falon wanda aka ƙayata da kujerun silba masu sulɓi suna sheƙi, ko ina shimfiɗe da marbles, ga ƙamshi ga sanyin iyakwandishin da ke ratsa ko ina, saboda duk baƙon da ya zo ya ji daɗin tarbar da aka yi masa.

Ganin ta wuce sumul ba tare da wani abin ɗaga hankali ba, ya sa ta kawo ajiyar zuciya ta sauke haɗe da lumshe idanu, ai kuwa kan ta buɗe su ta ji ta haɗu da wani abu mai tauri da ƙamshi da ɗumi, da sauri ta buɗe idanunta, gudun ko ta ji ciwo.

Ko me take tunani, ba ta ga abu a gabanta ba… Nan ta yi turus! Domin kuwa ba abu bane wanda dai take ta ƙoƙarin gujewa, shi ɗin ne ta faɗa kuma rigimarsa, domin ko ba ta faɗa ba, wannan kallon na tsantsar rigima ce a tare da shi, hakan ya sa ta kauce masa cikin sauri.

“Yi haƙuri!” Kawai ta iya faɗa, domin ba za ta ma iya ce masa Yallaɓai (Sir) ɗin ba, saboda dalilai masu dama.

“Idanun naki dama ba su gama warkewa bane, ki ka cire tabarau ɗin?” Ta san magana ya faɗa mata, amma ba ta nemi tanka masa ba, kafin ma ta ce wani abu ya ce, “Sannan, meye dalilinki na tauye min lokacina?”

A razane ta ɗago idanu aka yi rashin sa’a idanunsa tsab! A kanta suke, “Ko kuwa ƙarfe huɗu da rabi ki ka ji an faɗa miki shi ne lokacin tashi a aiki?”

A hankali ta sauke numfashi sannan ta ce, “Ayi min uzuri, ina da abu mai muhimmanci ne da ya taso min, shi ya sa.”

Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya haɗe ran nan, uwar haɗewa, sannan ya sa kai cikin falon haɗe da saƙala hannunsa ɗaya a aljihun wandon suit ɗinsa na Hugo Boss, yayin da ta samu daman shigewa, amma ba tare da ta gagara jin tasirin ƙamshin turarensa a cikin ranta ba, domin kuwa ƙamshinsa kaɗai ke sawa ta haukace idan ta tuno abubuwa da dama, bare aje ga idanunsa masu rigima.

Da ƙyar ta samu hannunta ya bar rawa har ta iya tada motar, ba wai tsoron Oganta ne ya haddasa mata wannan halin da ta faɗa ba, tsoron abinda Ogan nata zai iya yi game da ita, shi ya fi ɗaga mata hankali.

A gaggauce ta wuce cikin gida, sai da ta yi wanka ta shirya, sannan ta nemi Maami wacce ta baro a ƙasa, ita ma dawowanta kenan daga kotu inda take aiki a (Court of Appeal).

Ta fi minti goma a zaune a falon ba tare da sanin abin da ke gewaye da ita ba, har sai da Fa’iz ƙaninta ya yi mata ihu a saman kai, ya sa ta firgita za ta hau shi da faɗa ne. Fa’iz ya ce, “Adda Ummu, dole ya yi miki ihu ai, don kin yi nisa. Maami ke tambayarki ko kin bada saƙonta kan ki dawo?” Sai lokacin ta kula da Maamin ma a falon.

“Wai meke damuna ne?” Ta faɗa a ƙasan ranta, ɗaya zuciyarta ce ta ba ta amsa da, “Me yake damunki kuwa? Banda tunanin Zaid Abdur-Rahman?” Take ta ture wannan tunanin, “Allah ya sawwaƙa na yi tunaninsa, akan wane dalili? Mutumin da ya haramta gareni?

Ko bai haramta ba, da ni da tunanina mun yi masa fintiƙau, babu abinda zai sa tunaninsa ya zama halastacce a gareni. Saboda babu wanda na tsana duk duniya, irin sa.”

“Umm Aɗiyya lafiya ki ke kuwa?” Jin muryar Maami ya sa ta yi saurin yaƙe baki, cikin murmushin kawar da damuwar da take ciki ta ce, “Maami lafiya ƙalau, kawai dai na gaji ne. ”

“Sannu, ki huta mana sannan mu ci abinci.”

Shafa ɗan shafal ɗin cikinta ta yi, cikin yatsina fuska ta ce, “Maami ku fara kawai, a ƙoshe na ke.”

Kallon tsab! Mahaifiyarta ta bita da shi sannan ta ce, “Kin tabbata ba wani abu ko? Ba dai Za…” Da sauri ta kaɗa kanta ta ce, “Ba komai Maami. Ku ci bari na yi shirin sallah na ga maghrib, ya gabato.”

Ta daɗe tana azkaar, bayan ta idar da sallah, sannan ta sauko falon daga ɗakinta da ke sama, sai dai turus! Ta yi ganin mutanen falon, wani irin abu ne ta ji ya taso ya turniƙe mata zuciya yana yi mata ciwo. Daidai lokacin da abin tuhumar nata ya juyo suka haɗa idanu.

Tunda take, ba ta taɓa ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdur-Rahman ba. Ta so ta juya, amma ganin su Maami ya sa ta fasa, ta shigo falon ta gaishe su sama-sama, don tare suke da Yayanta Saadiƙ.

Har ma yana tambayarta, “Umm A. Da fatan dai waɗannan ba su ba ki wahala a wurin aikin?”

Murmushi ta yi har sai da kumatunta ya loɓa, sannan ta ce, “Mutanen da suka bi ni har da roƙo, saboda na yi masu aiki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, ai ka ga ba za su yi garajen ba ni wahala ba, don haka ina aiki na cikin kwanciyar hankali, with full amenities. Ko ba haka ba?” Ta faɗa cikin ɗan murmushinta haɗe da harɗe hannayenta saman ƙirjinta.

Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yake yi, “Saadiƙ, dole mu kula da Aɗiyya, saboda ko ba komai ta san yadda take amfani da ƙwaƙwalwarta, she’s very smart.” Ya ƙare maganarsa cikin murmushi.

Tsumewa ta yi haɗe da aika masa kallon banza. Dole ka ce ku na kula da Adiyya, banda ɗan karan wuyar da ku ke ba ni, me ku ke yi? Kullum na yi aiki, sai an ƙwaƙulo kuskure a ciki, ko me ya kai shi ɗauka na aikin ma tun farko, oho? Barin falon ta yi zuwa kicin, inda ta yi zamanta a can ta ci abincinta.

Bata sake bi ta kan falon ba, bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado sai aikin saƙe-saƙe take yi, abu ɗaya ke yawo a ƙwaƙwalwarta, kuma hanya ɗaya ce da za ta bi don magance wannan damuwar, ita ce ta bar aiki a AZ IT Consultants. A karo na uku!

Ko su kaɗai suke ɗaukar ma’aikatan da suka karanta fagenta, ta yafe wannan aikin da irin uƙubar da take shiga kullum wayewar gari. “To ma wai aikin dole ne?” Umm Aɗiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba, ta samu kanta tana tsiyayar hawaye. “Duk har da laifin Abba ma, yaya za ayi bayan na faɗa masa komai kuma ya ce na ci-gaba da aiki da su?”

************

Babbar yatsar hannunsa na dama yake kaɗawa kan sitiyarin motar, yana tafe yana tunanin abubuwa da dama. ƙwarai ya san cewa ba ƙaramin kuskure ya yi ba da ya sake barin Umm Aɗiyya ta shiga rayuwarsa.

Koda kuwa ta fuskar aiki ne, duk da kasancewar ba yadda za ayi ya yakice ta daga rayuwarsa, saboda abin da ya haɗa su ba ƙaramin abu bane da zai warware a dare ɗaya, abin da ya haɗa su dangataka ce da ba ta rabewa ba, a tunaninsa ya mance da ita, ya sa ta a gefe, ba za ta taɓa tayar masa da abubuwan da ya zaci ya adanasu ya ɓoyesu a wani lungu a can cikin ƙirjinsa ba, sai dai yau abin da ya gani a tare da Adiyya, sun motsa masa abubuwa da dama masu daɗi da masu ɗaci.

Amma ya zama dole ya dubi ɓangaren daya dace ya yi aiki da shi, saboda hakan zai fi fishe su, daga shi har ita. Har rana mai kamar ta yau ba zai taɓa mance abinda ya faru ba. Birki ya ja da ƙarfi, a dalilin wata motar da suka kusa yin karo, ashe tsabar tunani, ta sa ya bar kan hanyarsa ya hau wata daban.

“Zaid Abdur-Rahman ka wuce haka!” Ya faɗa a bayyane, yayin da ya yanki kwanar (Darussalam Close da ke Wuse 2), inda shiryayyen gidansa yake.

***********

Zaid Abdur-Rahman Nafaɗa ɗa na uku a cikin yara goma sha bakwai wurin mahaifinsa, mutum ne da ya taso cikin gatansa dai-dai gwargwado, mutum ne kuma da ya saba samun duk abin da ya nema, ko ya yi burin samu, saboda hazaƙarsa da kuma jajircewansa.

A garin Gombe ya yi ƙaramar makarantarsa kafin ya wuce zuwa sakandirensa a birnin tarayya Abuja, a Kwali. Wannan ya yi mafarin zamansa gidan Baffansa ƙanin mahaifinsa Builder Zubair Nafaɗa.

Tun daga lokacin kuwa zaman shi ya fi yawa a hannun ƙanin mahaifin nasa, don ba kowane hutu ma yake zuwa gidansu ya yi ba. Sai a nan Abuja yake hutunsa. Koda ya tashi tafiya jami’a. Baffansa (Abba) ne ya yi masa duk wani abin da ya dace har ya wuce India, inda ya karanci aikin Injiniyar sadarwa. (Telecommunications Engineering).

Kallo ɗaya za ka yiwa Zaid, ka fahimci shi ba mai yawan magana bane.

Bayan ya kammala karatunsa  na digiri ne, ya wuce karo ilimin Masters ɗinsa inda ya tafi jami’ar Hertfordshire da ke United Kingdom, duk dai kan IT, ya karo ilimin.

Mutum ne wanda ya riƙi neman ilimi da tsantsar muhimmanci, haka nan yana da karambani wurin yawan bincike da nemo sabon abu, wannan ya sa ya yi suna har ya yi fice. Dalilin haɗuwarsa da wani bayarabe ma kenan wurin wata gasa ta ƙasa har suka zamo abokai.

Kowa yana inda yake, yayin da Zaid yake aiki da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta ƙasa. Femi yana aiki a Warri, amma a hankali suka zame suka tada wani ɗan kamfaninsu na gina Softwares da kuma ƙera gamayyar kwamfuta (Hybrids), a hankali abinsu na bunƙasa har suka gamu da wani mutumin Adamawa Sufyaan. Shi ma ya zuba hannun jarinsa, aka ci-gaba da tafiya, ga shi yanzu bayan watsa kayan kamfaninsu da suke yi cikin ƙasa, suna shigo da na waje, sannan suna bada shawarwari wa masu neman shawara .

Wannan ya sa suka yi fice kan ka ce meye (AZ IT Consultants), ya yi suna a faɗin ƙasar, don ba inda ba su shiga domin hada Networks da kuma ƙaddamar da sabbin Softwares, kama daga bankuna da kamfanoni, asibitoci zuwa ma’aikatu da kuma kafa na’urar tsaro na kamfononi da ma’aikata har ma da gidaje.

Zaid Abdur-Rahman mutum ne tsaurarre da ba ka taɓa gane alƙiblarsa kuma mutum ne murɗaɗɗe, idan ba ka yi sabo da shi ka daɗe da fahimtar cewa hakan yake ba, za ka ɗauka ba wanda ya kai shi faɗin rai. Wannan ya sa duka abokan kasuwancinsa guda biyu suke mamaki, idan suka samu abokin ciniki, (Client) ta dalilin Zaid.

Ganin kamfaninsu ya bunƙasa ya sa suka yi masa tsari na zamani suka samu ofishi na musamman suna kuma ɗiban ma’aikata, har makarantar horar da mutane kan harkar ƙera Softwares da kula da Komfutoci, (Maintainance), suna da shi a wannan kamfanin. Yanzu shekaru bakwai kenan da fara wannan harkar tasu.

Yawan kamewarsa ce ta sa bai ganin amfanin ma ya tsaya wai bin mace, tana ba shi wahala. Wannan ya sa shi sam mata ma ba su gabansa bare wata aba wai soyayya. Soyayyarsa ɗaya ce, ita ce ga Komfutarsa. Idan har ka ga yana sakewa mutum fuska, to ‘yar-uwarsa ce, mutum ɗaya ce jininsa ya haɗu da nata wato Asma’u.

Abinda ya sa kuma ba ta ɗaukarwa kanta halayyar shisshigewa ɗa namiji ba, sannan kuma tana da gudun zuciyar mutum. Tun tasowarta yake kulawa da lamarinta, domin tasu ta zo ɗaya.

************

          BABI NA BIYU

Umm Adiyya Zubair, yarinya ce mai kimamin shekaru ashirin da huɗu a duniya. Ita ce ‘ya ta huɗu wurin iyayensu. Bldr. Zubair Nafaɗa da kuma Justice Khadija Muhammad, wacce suke kira Maami haɗe da jan ‘Maa’ ɗin Maamin.

Idan ana kiran kyawawa, sam Umm Adiyya ba ta saka kanta a cikinsu, amma kuma duk wanda zai ganta a gefe da irin yanayin kyawun da zai siffanta ta da shi. Ba ta da tsawo, idan banda kyawun dirinta ma, mutum ba zai ba ta shekarunta ba, idan ya yi mata ganin farko. Fara ce sol! Kuma tana da cikakkun ƙugu, wanda ya tafi daidai da yanayin jikinta na mai ƙaramin ruwa.

Kallo ɗaya za kai mata ka san cewa ita cikakkiyar bafulatana ce, domin hatta gashin kanta yauƙi da tsawo yake da shi, ga wadataccen gashin gira da ƙaramin baki, sai madaidaita idanunta, wanda suke ƙunshe da wani annuri, kullum farare tas! Za ka gansu, ba ta da dogon hanci irin dai na Fulani, amma yadda take da ƙaramar fuska haka madaidaicin hancinta ya dace da ƙaramin bakinta da ya zauna a fuskarta.

Ba ta cika son hayaniya ba sam, kuma akwaita da ƙwazo da hazaƙa, domin yanzu haka ta kammala karatunta a ɓangaren Engineering, inda take da digiri a (Electrical Electronics Engineering), kowa yana mamakin zaɓin wannan ɓangaren na karatun nata, ganin ta na ‘ya mace, yawanci mata sun fi son kos masu sauƙi.

Amma kuma haka zalika kowa ya san za ta iya, domin Umm Aɗiyya tana da ƙwaƙwalwa sosai, ga shi ta gamu da iyaye masu ɗora yaransu kan tsari na ilimi na boko da na addini, don hatta Maami ba ta da wasa. Ba a batun Abban su kam, da ba daman ya shigo gida ya ga babu littafi a hannunsu, sai sun samu rabonsu.

Yaya Saadiƙ shi ne babban yayansu, sai Adda Zubaida wacce ta yi aure tana zaune a Bauchi. Adda Asma’u ke bin Zubaida, sai Umm Adiyya da kuma ƙannenta maza Fa’iz da Faruƙ ‘yan biyun su.

Yaya Saadiƙ a garin Gombe yake aiki da Branch na PenCom, wanda yake can, sai Asma’u wacce ita kuma da AZ IT take aiki a nan Abuja. Inda suke da zama, a halin yanzu ma aurenta ake shirin yi, wanda shi ne musabbabin juyewar duniyar Ummu A. kamar yadda suke kiranta wasu lokutan.

Duk da kasancewarta shiru-shiru. Allah ya bawa Umm Aɗiyya tarin masoya ta ko ta ina, domin tun kan ta gama karatu, iyayen kansu sun zaci za a samu wanda za ta gabatar a cikin maneman nata, tun suna zuba mata idanu, har suka ga abin ya yi yawa suka sa ta a gaba da tambaya, amma ta nuna masu ita babu tukun na. Har suna tunanin haɗata da ‘yar-uwarta su aurar  da su tare, sai ga shi bayan shekaru uku Asma’u za ta yi nata auren, amma Umm Adiyya shiru.

Maami ta sha ajiyeta ta sa ta a gaba da tambayoyi, amma kullum amsar ɗaya ce, “Maami babu dai tukun na, komai lokaci ne.” Don haka Maami ta ƙyaleta.

************

SHEKARU BAKWAI DA SUKA WUCE

ABUJA, (2003)

Wata ranar Litinin ta fito da ƙawayenta Nazira da Suwaiba za ta rako su mota, bayan sun gama bitan karatunsu na jarabawar da za su soma na (WAEC), a cikin satin, shi kuma ya iso gidan. Har ga Allah fitowarsa daga mota da ta gan shi, sam ba ta san me ya same ta ba, illa iyaka sai ji ta yi su Nazira suna cewa, “Kar ki manta ki fito da wuri goben.”

Yaƙe ta yi masu kawai, saboda har zuwa lokacin, ji take yi kawai gabanta na dukan uku-uku. Na farko dai ba yau ta fara ganinsa ba, na biyu kuma ba yau ta fara ganin kyakkyawan namiji ba, amma ta rasa me ya sameta da ta yi masa kallo guda! Ta sa kai za ta koma cikin gida ne ya ce, “Ke Aɗiyya, ba kya ganin mutane ne?”

Jikinta na rawa ta ce “Yaya Zaid, sannu da dawowa”

“Haba, ko ‘yan makwaɓta dai suka ganni sun san su yi farin-cikin ganina bare ‘yar ƙanwata, shekara nawa? Shekaru biyu ƙwarara ba ki ganni ba, iya murnan ki kenan? To na ajiye ki a gefe, daga yau Asma’u ce mutumiyata.”

Murmushi ta yi ta rufe fuskarta sannan ta ce, “Sorry, Yaya Zaid.” Sannan ta miƙa hannu za ta karɓi jakar hannunsa wacce ta fi kama da ta komfuta, da sauri ya janye ya ce, “Je ki abinki, na hutasshe ki, su Fa’iz za su tayani.”

Ai ba ta ida rufe baki ba, suka tunkaro su, cikin murna da hayaniya, wannan ya sa ta koma ciki jiki a sanyaye, har dare ranar ta kasa sanin abu guda da yake mata daɗi, lokacin ba ta danganta shi da ganin Yaya Zaid ba, saboda ita daman ba wani sabo take yi da mutane ba, saboda shirunta ya yi yawa.

Tana ganin yadda kowa ya damu da shi, don ko wurin iyayenta idan ba tsoron ƙarya ba, sai ta ga kamar sun fi ji da Yaya Zaid akan su. Kwanakin shi biyu da dawowa, ya tafi Gombe wurin iyayensa. Umm Adiyya kuwa ta maida kai haiƙan wurin karatunta, dama ba tayar baya bace.

Ita har ta manta da zancen Zaid, saboda ya ɗauki satuttuka kafin nan ya dawo. Ai kuwa bayan ya dawo, da gaske yake yi ya share ta, domin sau goma zai in aike, to Asma’u ko su Fa’iz yake sawa.

Wani baƙon al’amari a gareta shi ne, duk inda aka ambaci sunansa a gidan, to tana sauraran ta ji me za a faɗa, saboda haka kawai hira idan dai ta Zaid ce, to yana sa ta nishaɗi. Idan kuwa ta gan shi, sai gabanta ya yi wannan faɗuwar.

***********

Tana cikin karatu da yamma a falon Abba, kasancewar duka ana hira a falon Maami ne, ya sa ta zaɓi nan saboda ta samu natsuwa, ba ta san hawa ba bare sauka, ta ji an cire mata littafin daga hannunta.

“Adda Asm…” Ba ta ƙarasa ba ta yi dif! Saboda koda wasa ba ta yi tunanin shi bane, “Har za a yiwa Adda Asma’u masifa, oya ci-gaba ina jinki.”

“Ba masifa fa zan yi ba Yaya Zaid.” Ta faɗa a cikin muryarta ta shagwaɓa.

“Ba surutu na ce ki min ba, karatun za ki min.” Nan ne ya duba abinda take nazari, nan take kuwa ya jefo mata tambaya.

Ganin haka, ya sa ita ma ta ba shi amsa yadda ya dace, sun daɗe suna haka daga baya ya ce, “Good, ina son haka, tunda kin gane sai ki huta, kuma anjima idan ki ka ɗaga, sai ki ji kin ƙara fahimta.”

“Na gode.” Ta faɗa ƙasa-ƙasa, duk yadda yake shige mata, wataran ya zolayeta, ita kanta ba ta taba ruɗin kanta ba, domin ta san Yaya Zaid ba abinda ya tsana irin raini ko kuwa wasa, don kaf! Dangi ma ita da Asma’u ne suke cin arziƙin ya yi masu wasa. Hakan ya sa ta kama kanta, muddin ba shi bane ya fara janta da irin wannan ba ta taɓa yi masa iyakacin su gaisuwa.

Bayan sun gama ne, wayarsa ta yi ƙara wannan ya sa ya miƙe, domin amsa wayar, binsa ta yi da kallon tsaf! Koman Yaya Zaid kyau yake mata, muryarsa wanda take mai zurfi a murje, tamkar wanda ya yi kos wajen fidda sauti mai daɗi. (Deep Smooth Whisper-Like Voice).

Yanayin yin abubuwansa da komansa cikin natsuwa yake yi, siriri ne ba shi da ƙiba, haka nan dogon fuska gare shi, wanda dogon hanci ya shimfiɗu a kai, yana da tsawo. Domin idan ka dubi Umm Aɗiyya, ka dubi Zaid to za ka ga cewa koman su ya sha banbam, saboda hasken Zaid ba fari bane tas! Zama a fi jera shi a sahun bakake. Gashin kansa ne kawai irin nata, wanda yake a kwance kamar na jarirai.

Haka take zaune har tsawon minti ashirin, sai da Faruƙ ya shigo falon, sannan ta dawo hayyacinta ta kula da iya tsawon lokacin da ta ɗauka tana tunani. Ba ta yi aune ba, son Zaid ya shige ta faraɗ ɗaya, domin ba ta san so bane, sai da ta yi nisa sosai. Shi kuwa tsakaninsa da ita aika da karatu, baya ga haka, ko hira ba su yi.

A wannan yanayin ta kwashe shekara guda cikin soyayyar ɗan-uwanta wanda bai san tana yi ba. Zuwa lokacin adimishan ɗinsu, har ya fito ta fara karatunta a (A.T.B.U Bauchi), ganin Adda Zubaida ta yi aure anan, ya sa abin ya zo da sauƙi. Tafiyarta makaranta ne ya ɗan rage mata abubuwa, saboda rashin ganinsa ya sa ta samu sassauci, duk da kuwa ta yi sabbin manema a Bauchi, ba ta ba su fuska ba.

Tun dawowar Zaid daga karatu, shekaru biyu kawai yayi yana aikin gwamnati, kafin su haɗa kai shi da abokansa biyu, su buɗe kamfaninsu na na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Wannan aikin ne kusan ya canza Zaid daga Zaid ɗin da, domin kuwa sai ya zamana babu wani abin da ya sa a gaba, sai (AZ IT Consultants & Services.) Abu ya haɗu da albarkar iyaye, sai haɓɓaka yake yi, babu kama hannun yaro.

*************

ABUJA, 2005

Yana zaune a cikin Apartment ɗin da Abba ya ware masa, yana duba wasu rahotanni da wani ma’aikacinsu, ya shiryo ne, wayarsa ta ɗau tsuwwa, bai da niyyar amsawa, amma da ya ga fuskar wayar, nan da nan ya amsa.

“Haba dai Sweetheart, kuma haka ake yi ne? Sai ki share ni, don kawai kin tafi Sakkwato?”

Asma ta yi dariya ta ce, “Haba Yaya Zaid kuma idan na share ka, ai kai me nemo ni ne, ka ji ko, lafiya.”

“Uhm da wannan ma don wannan, ayyuka ne suka sha gabana. Yaya karatun dai?”

“Karatu, Alhamdulillahi, amma ya ɗau zafi.”

“Haka ne daman ai, Allah dai ya taimaka, sai fa kin dage, don na ji labari Umm tun tafiyarta first class, take ja, idan ki ka yi wasa, za ta fi ki ƙoƙari.”

“Kai rabu da ƙwaƙwalwar Ummun nan, wa zai iya Competition da ita? Ai sai mutum ya kar kansa.”

Dariya ya yi ya ce, “Duk ƙaton kan nan naki, ki ce ba ki da irin ƙwaƙwalwar Ummu? Ita fa saboda tsabar ƙanƙanta, hatta kanta ma ƙarami ne.”

“Idan ta ji-ka dai tsakaninku, na gaisheka. Yaya Zaid banda credit.”

“Yau kam tunda kin kyauta, kin kirani kin cancanci Recharge card, na san sha’anin Students.”

“Kai amma da ka kyauta min kuwa sosai, na gode. Ina saurare.”

Murmushi ya yi suka yi sallama, yana tunani a ransa, daga bisani kam kashe komfutar ya yi, sannan ya fito ƙofar Apartment ɗin, wanda yake cikin katanga ɗaya da gidan Abba a unguwar Maitama. Domin haka nan ya samu kansa a cikin nishaɗi.

Ai ko Asma’u ba ta matsa a wurin ba, ta ga ya yi mata transfer ɗin katin waya na dubu biyar.

*************

BAUCHI 2008

Ranar da ta kammala jarrabawarta, ta haɗa jakarta tsab! Adda Zubaida kam tana ganin ikon Allah, “Yanzu Ummu A. Ba za ki ɗan yi mana hutun bane za ki yi gaba?”

“Zan dawo saura sati a fara karatu, yanzu kam Allah ya gani na yi kewar Maami sosai, kuma ke ma kin san don gidanki na ke, da kin ga sawunta a nan.”

“Hmmm! ‘Yar Maami kenan, kamar ke ce autan ma ba Twins ba. Na amince ki tafi, amma ana saura sati biyu hutu ya ƙare, zan kiraki na yi miki tuni.”

“Ah, Adda Zubaida sati biyu ya yi yawa ai. Ina laifin kwana biyar?”

“Cuwa-cuwa kenan, anya ba wani catch aka yi a Abujan nan ba ake ta saurin tafiya?”

Nan da nan Umm Adiyya ta ɓata rai, “Wuuu! Rufa min asiri. Allah ya suturu bukwui, yau me ya kai ni? Inji da damuwar kaina mana.”

Adda Zubaida na dariya ta ce, “Ke dai Allah ya shiryeki. Wallahi, sai ki ci karatun ai. Muna nan da ke, sai mun samo miki miji ai.”

“Wai, ina ce haka ku ka bar Adda Asma’,  ni meye  ya sa ku ka sa min idanu?”

“Wai ma ki bar ruɗin kanki, domin na san Abba haɗaku zai yi idan ya tashi, ba sau ɗaya ba, na ji yana faɗin hakan, don haka tun kafin ta fidda gwaninta, ke ma ki riƙe naki a hannu.”

“Kar ki damu, zan jira har ta samu nata tukun.” Zubaida dai dariya kawai ƙanwar tata take ba ta, domin da an mata maganar aure, to tamkar an kawo labari mai ban tsoro ne, nan da nan za ta ture shi a gefe, ita a tunaninta don ba ta ga wanda take so bane, a rashin saninta, tsoron fitowar soyayyar wanda take so ɗin, ya sa koda yaushe take janyewa tattaunawa akan wannan maudu’in.

Ba ta tashi shiga tashin hankali ba, sai da mai ɗaukarta ya iso, don koda wasa ba ta taɓa tsammanin shi za ta gani ba, ita dai sun yi da Abba za a taho yau washegari su kama hanya. Don haka ganin Yaya Zaid ya ba ta mamaki ƙwarai, yaya aka yi ya bar duka ayyukansa, don ya zo ɗaukarta?

“Umm A. Magana dai Yaya Zaid yake miki kin yi shiru.” Adda Zubaida ce ta yi magana, wannan ya sa ta ɗago a firgice. “Na’am Yaya.”

“To ko dai EE ɗin ne suka fara juya maki ƙwaƙwalwa tun yanzu?”

Kanta a ƙasa, ta ɗan yi murmushi, “Ki shirya wai ku tafi, zai gaida su Baffah Abdu a Gombe sannan ya koma, ko za ki jira shi sai ya dawo ku wuce?”

“Me za ta zauna ta yi? Ba sai mu je ta gaishe su ba, ki na ganinta, ba ta son zumunci. Baƙin halinta ya yi yawa, ba ta son mutane.” Gaba ɗaya sai ta ji nauyin shi, ganin har ya gano, ita ba mai son mutane bane. Duk da dai ba wai ba ta son mutanen bane, ita dai ba ta sakewa ne da mutum, idan jininsu bai zo ɗaya ba.

Tana ji, tana gani, ya sa ta shirya suka kama hanyar Gombe, ita tsoronta ɗaya, kar ta yi wani abu, ko ta ce wani abu da zai sa ya ganota, don muddin ya gane tana sonsa, ta san za ta sha wulaƙanci, don haka take samun labarin masu nuna soyayyarsu da farko wa saurayi suke fuskanta, mafi yawan lokuta.

“Yaya ki ka yi shiru? Sanyi ki ke ji ne?”

“A’a”. Ta ba shi amsa a taƙaice, duk iya ƙoƙarinsa na ganin cewa ta sake ya gagara, to shi ɗin ma daman ba wai hirar bace ta dame shi, yana da abubuwan da suka wuce wannan, don haka ya yi shiru ya bar ta, har isar su.

Yau ma gidan a cike kamar ko yaushe wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ba ta cika son zuwa ba saboda hayaniya, amma kuma idan tana cikin ‘yan-uwanta, ta kan ji daɗin yadda suke ƙaunar junansu.

Alhaji Abdur-Rahman Nafaɗa, matansa na aure uku ne, wannan ya sa yake da yara da yawa, don ɗakin su Zaid ma su biyar ne. Zaid shi ne na uku, ya biyo Yayan shi Nazif, sai babbar yarsu Sa’adiyya, ɗakin Anty yaranta shida. Sai Umma wacce take da yara shida ita ma. Don haka ba ka raba gidan da yara, duk da dai ‘yan matan sun yiyyi aure, akwai ‘yan mata uku, sai samarin gidan.

“Wai lallai yau Zaid ka yi abin arziƙi, Umm Aɗiyya ka ɗauko mana? Shi ya sa na hango hadari ɗazu ta gabas ɗin nan.”

Duka jama’ar falon suka sa dariya, bayan sun ji bayanin Anty. Kunya duk ta rufeta ta ce. “Anty, ai ina son zuwa, ba na samun lokaci ne, da zarar an koma, to karatu da zafi-zafi muke yi.”

“Ayya, to Allah ya taimaka.”

“Maryam, samo masu abinci da abin sha daga falon Babanku, na san can kam ba za a rasa ba, kun yi tafiyar yamma.”

Umm Aɗiyya kam ta san ba yunwa take ji ba, sai dai ba yadda za ta ce su bari, shi ya sa ta yi shiru. Muryar Zaid ta ji ya ce, “Kai! Anty abincin kun nan ku bar shi kawai sai dai na dare, ni dai ba ni jin yunwa, sai dai ko Ummu?” Ta ji mamakin yadda tunaninsu ya zo ɗaya, sai murmushi ta yi.

A hankali ta girgiza kanta. “Kai dai ka hanata ci, ai da ba ta ce ba ta so ba, sai da ka yi magana. Rabu da shi, kar ki biyewa ɗan gidan kun nan, ya iya baƙin hali. Maryam tafi ki kawo mata.”

Ganin ta dage, ya sa ta haƙura aka kawo abincin, amma ɗan kaɗan ta ci, sai kunun aya ne mai sanyi ta sha sosai.

A falon cikin gida aka haɗu da dare aka yi ta hira, sai ga Umm Aɗiyya da dariya, saboda sai dai ba ka zauna da Umma da Anty ba, sai ka ci dariya, Mama kam tana gefe ba ta shiga sha’aninsu.

Wai saka yaran suka yi a gaba, sai dai su faɗa masu wacce tafi kyau. Duk abin nan da ake yi, hankalin Umm Aɗiyya na kan Zaid da ke zaune kan kujerar zaman mutum ɗaya, yana ta danna waya, da ta ga zai ɗago ido, sai ta maida ganinta wani wurin daban.

Washegari da sassafe suka ɗauki hanyar Abuja, sai dai yau ita ma ta shafawa kanta lafiya, tun da suka fara tafiya, ta sa gyalenta a saman fuska tana kallon windo, ta lumshe idanunta tamkar ta yi barci. Kasancewar sun samu waya, an kwana rikici a Riyom, ya sa suka ɗauki hanya ta Kano. Har shigar su Kano, ba ta motsa ba, duk (Check Point), da za su zo, bai sa ta buɗe idanunta ba.

Duk rashin son hayaniyar Zaid, sai da shirun Umm Aɗdiyya. Ya dame shi, “Wai gum aka saka miki a bakinki ne hala?” Shiru ba ta ce komai ba, sai da ya nanata tambayarsa, sannan ne ta juyo ta kalle shi, suna haɗa idanu, ta sauke ganinta, “A’a kawai dai…”

“Kawai dai, ban iya hira mai daɗi ba ko?” Ya tambaya idanunsa a kan titi.

Da sauri ta ɗago ta dube shi, ƙwarai ta ji mamakin tambayarsa, “Yaya Zaid hira mai daɗi kuma?”

“Na yi ta miki magana tun ɗazu, amma kin yi nisa. Ba dai saurayi ki ka yi a Bauchin ba, ki na tunanin tafiya ki bar shi? Anya ma ki na karatun kuwa? Zan yi magana da Zubaida, ta sa miki idanu sosai, daga yin Session ɗaya kin fara zurfi a tunani, ina labarin sauran shekaru huɗun kuma fa?”

Gaba ɗaya sai ta ji maganar banbaraƙwai, wai namiji da suna Hajara, ita tana can tana ta fama da ciwon sonsa, shi yana tunanin har ma tana da wani saurayin da za ta iya ɓata lokacinta a kan tunaninsa? Har da wani yi mata faɗa. Hawaye ne ta ji sun ciko mata idanu, da sauri ta kau da kanta gefe, ta shiga gogewa a dabarance.

Shi ya zaci maganar da ya yi mata ne, ya sa take hawaye, don ya ga lokacin da ta goge hawayen haɗe da ɗan jan hanci kaɗan.

“Ko dai mu koma Bauchin ne, sai na ce da su Maami ‘yarsu kam ta yi masu bye-bye. Ta samu wanda ya sace mata zuciya.”

Dariya ta yi, don yadda ya yi maganar ta san zolayarta yake yi. Haka dai suke magana jifa-jifa. Can shi ma ya yi shiru, lokaci-lokaci yana amsa waya. Ba ta taɓa wahalalliyar tafiya ba irin ta ranar. Amma kuma ko ba komai ta ƙara samun lokaci da Yaya Zaid, wanda ya fi mata komai daɗi.

Wannan hutun gaba ki ɗaya ta yi shi ne cikin jin daɗi, saboda falon Abba dai shi ne wurin zamanta, ta fake da kallon labarai, amma haƙiƙanin gaskiya shigowar Yaya Zaid kawai take son gani. Dawowar Adda Asma’u daga Sakkwato ne ya ƙarawa gidan armashi.

Wannan ya sa sam Umm Adiyya ba ta so ƙarewar hutunsu ba, amma lokaci na yi, haka ta tattara ta koma Bauchi. Ranar kamar anyi mata mutuwa saboda ta so ƙwarai Yaya Zaid ya ce zai maidata, amma ba ta gan shi ba ma ranar tafiyar, bare su yi sallama, don haka koda suka isa, haka ta kashe dare cikin tunani tana kuka.

A wannan daren ne ta ɗauki ɗabi’ar tsayuwar dare, koda damuwa ko babu za ta tashi bare tana da babbar matsala, soyayyar Zaid. Kullum tana cikin addu’ar neman zaɓin Allah da kuma mafita.

Da yake a Hostel take zama, sai Weekends take zuwa wa Adda Zubaida, sam Adda Zubaida ba ta karanci halin da take ciki ba, sai ma ta maida hankalinta kan karatu tuƙuru, bare ma aikin Lab. Da ake ɗibga masu, baya barin mata lokacin tunani, ga Assignment ga Lab. Reports, duka sun haɗu mata. Wasu lokutan ko sha’awar zuwa Weekend ɗin ma ba ta yi, saboda abubuwa sun cunkushe mata.

************

“Baban Walid, ni kam ka duba min Ummu A, gaba daya ta canza banda yawan tunani babu komai a gabanta.”

Umm Aɗiyya ta yi murmushi ta ce, “Baban Walid don Allah ka bar Adda Zubaida, ita wai ba daman mutum ya yi shiru, sai ta ce yana tunani.”

Dariya ya yi ya ce, “Ki bar ta tana meditating ne saboda ƙwaƙwalwar ta sha iska, ke kin ɗauka kowa ne irin ki?”

Kallonsu kawai take yi tana murmushi, saboda yadda rayuwarsu yake burgeta, ba wanda zai yarda cewa shekaru huɗu da suka wuce, a waya suka haɗu, bayan ya kira wrong number. Akan su ta ƙara yarda da maganar nan da ake cewa, matar mutum kabarinsa. Ga shi yanzu ɗansu daya har na biyu na kan hanya. Wannan ya sa wataran ba ta damun kanta kan Yaya Zaid, saboda ta san idan mijinta ne, shi ma wataran zai so ta.

Ranar Asabar suna tafiya da ‘yar ɗakinsu Taƙiyya sun fito daga NLT karatu ne. Taƙiyya ta ce, “Umm Aɗiyya na manta na faɗa miki gobe su Ahmad fa za su isa gaisuwa wurin su Baba.”

Da sauri ta dubeta ta ce, “Haba dai! Kai Allah ya sanya alkhairi, wai finally Ahmad sarkin naci dai shi ya yi nasara.”

“Ai na faɗa miki, ba don nacinsa ba, da sai dai ya ƙara gaba, don na sha sallamarsa, amma yana nan ƙememe.”

“To yanzun me ya canza miki ra’ayi?”

“Kin ga duk iya shegen da na ke masa? Bai taɓa gajiya ba, kuma na san so yake min tsakani da Allah kuma ni ma shi na ke so, don haka na ga ba amfanin ɓata mana lokaci, kawai dai ya faye matsi ne.”

Murmushi ta yi da ta tuno kanta, da za ta samu ita ma wanda take so ya so-ta kamar hakan da ba ta da damuwa. Amma kowa da ƙaddararsa.

“To Allah ya tabbatar da alkhairi, ya kuma nuna mana lafiya.”

“Ameen, saura ku.”

“Wuu! Ai mu kam ba yanzu ba, ai zan haukace idan na haɗa family da wannan baƙar wuyar da ake ba mu.”

Taƙiyya ta yi dariya ta ce, “Wai, baƙar wuya.”

“Dole ki faɗi haka, ke da ki ke EMT ba ki da matsala, amma ki na ganin yadda muke shan wuya a Complex.”

“Allah dai ya sa a ƙare lafiya. Kar ki manta fa ku ne ‘yan VC’s list.”

“Hmm, wannan zangon, idan na ci sa’a ne ma a tsinto ni a HOD’s list.”

“Haba ke kuwa kar ki karaya mana, a taimaka dai a dage.”

Suna shiga ɗaki. Saudat ‘yar ɗakin su ta ce, “Umm Aɗiyya, ɗazu kuna fita, ki ka yi baƙo, aka turo nemanki, don sun buga, wayarki a kashe.”

Juya idanunta ta yi cikin jin haushi, ita ta tsani baƙin naci, daga ji ta san wannan Ibrahim ɗin ne, tsaki ta ja ta ce, “Can masu.”

“Sun bar saƙo, wai na ce miki yayunki ne daga Abuja, amma sun wuce Gombe, idan suna da time za su duba ki, akan hanyarsu ta dawowa.”

Da sauri ta juyo, saboda ta ji an ce yayyinta, wannan yana nufin Yaya Saadiƙ da Yaya Zaid kenan. Maza ta yi ta karɓi envelope ɗin hannun Saudat. Kuɗi ne a ciki dubu ashirin, sai ‘yar takarda, (Note), an yi rubutu mai kyau, ko duba biyu ba ta buƙata, ta san mai rubutun, don kullum sha’awa rubutun ke ba ta, a cikin cursive handwriting yake rubutunsa.

 

“Mun shigo ba mu sameki ba, ga wannan ki sa kati, ba yawa, next time Inshaa Allah. Take care.”

Zaid Abdur-Rahman & Saadik Zubair.

 

Ranar ta karanta takardar ya fi sau ashirin, tana shafa rubutun tana jin ƙamshin takardar. Har takardar ta soma tsufa. Wannan ya sa ta haƙura ta yi masu kyakkyawar ajiya, daga takardar har kuɗin.

Murna da ƙyar ya bar ta, ta iya barci ranar, sai dai ta ji haushin rashin haɗuwarsu. Sai Allah-Allah take yi su biyo cikin makarantar a komawa. Sai da ta makara, washegari saboda rashin barci da wuri, tana gama cajin wayarta ta nemi Yaya Saadiƙ.

“Ke Mango Park mai kashe waya, ina ki ka shiga?”

“Hmm! Yaya Wallahi ina NLT na je karatu, ai na ji haushi da ba ku sameni ba, na ga saƙo fa, na gode.”

“Ba komai, Yaya Zaid ne ya ba ki. Call him.”

Ai nan ta haɗiyi wani abu makut! Saboda tana da lambar wayarsa, amma ba ta taɓa kirarsa a waya ba, saboda abinda muryarsa ke mata a cikin ƙwaƙwalwarta da ilahirin jikinta.

“Yaya kawai ka faɗa masa, daga baya zan kira shi, yanzu an mana fixing lectures, kuma na yi latti, sai ƙarfe ɗaya kuma za mu fito.”

“To shi kenan, ga shi nan ma ya shigo ku yi magana.”

Ai kafin ta ce masa, a’a tuni har ya miƙa masa wayar. Idanunta a runtse ta buɗe su a hankali, “Hello, Assalamu-alaikum. Ina kwana… ina wuni… an kwana… Yaya Zaid?” Gaba ɗaya ta faɗa a jere haɗe da make goshinta cikin takaici.

“Lafiya ƙalau, yaya karatu?”

“Alhamdulillahi.”

“Kin ci sa’a jiya, na samu shaida, ki na karatu da na samu akasin haka, da na gamu da ke.”

Murmushi ta yi ta ce, “Yaya na ga saƙo na gode, Allah ya biya da mafi alkhairi.”

“Ah, ba komai. Ameen-Ameen. To Sai anjima ko? Take care.”

Wai! Ai tamkar ta kusa shiga aljanna, tsabar daɗin kalamansa, ga shi har bayan sun gama wayar, dirin muryarsa bai bar kunnuwanta ba.

Ashe ta riƙe wayar a wuyanta, ta rungume sai murmushi take yi, ba ta sani ba, buɗe idanun da za ta yi, kawai ta ga su Taƙiyya a gefen gadonta sun zuba mata idanu, tana ganinsu, suka sa mata dariya.

“Yau kam za ayi ruwa da ƙanƙara, asirinki ya tonu, wannan dai mun san ba Yaya bane Yaaaya ne ko?” Suka faɗa suna mata tsiya, rufe fuska kawai ta yi tana murmushi.

************

Lokacin ne ta ƙara samun natsuwa wurin yin karatun ma. Hutun da suka yi na gama aji uku ne, ya yi daidai da lokacin tafiyar Adda Asma’ Service, su Abba dai suka yi mata cuku-cuku, aka turata Abuja, ai ko nan da nan ta jona bautar ƙasarta da wurin su Yaya Zaid, don tun ba yau ba, ta matsa masa akan wurinsu take so.

Har ma yake ce mata, “Ba ki na murna ba, aiki za ki yi kamar kowa, wurin mu ba wasa.”

“Eh, na yarda.” Ta faɗa a gaggauce.

“Anya ba kuɗin da muke biya ki ke so ba Asma’, wannan irin ɗoki haka? Bari za mu rage kuɗin Co-members, wannan shekarar.”

“Ah, don Allah Yaya ka yi haƙuri.”

Girgiza kai kawai ya yi ya ce, “See her! To na ji, shi kenan.”

Umm Aɗiyya tana zaune suka yi wannan maganar, amma ba ta buƙatar kowa ya faɗa mata komai, domin kuwa tunda take da Yaya Zaid, bai taɓa mata yadda yake yi da Adda Asma’ ba, sannan ba ta taɓa ganin yanayi wa kowa kallon da yake yiwa Adda Asma’ ba.

Da gani ba tambaya, ka san kallon da yake yiwa Asma’ daban ne da kowa. Wannan tunanin ne ya fara wargaza mata ƙwaƙwalwarta a karo na farko. Kar dai Yaya Zaid son Adda Asma’ yake yi?

***********

Sun yi shirin kwanciya barci ne washegari. Asma’ ta buɗe wardrobe ɗinta ta fito da wani setin turare na smart collections a cikin farin kwali take nunawa Umm Adiyya haɗe da wasu kayan maƙulashe dangin su Assorted Chocolates.

“Ummu A. Tashi ki ɗebi naki, ɗazu aka ban gift, ni ban san yadda zan yi da su ni kaɗai ba.”

A take ta zabura ta zauna tana kallon kayan, jikinta ya hau ɓari, har ga Allah ta yiwa ‘yar-uwarta murna ta samu wanda take so, yana sonta, amma da ganin kayan ta tabbatar da zarginta, tabbas Yaya Zaid sonta yake yi, idan banda haka, namiji bai taɓa baiwa budurwa kyautar su turare ba, sai idan ya yaba, yana so ko kuma suna soyayya.

“Adda Asma’ ki ɗauka kawai duka, kin ga musamman aka ba ki, zai fi dacewa ke ki yi amfani da su, shi ma zai fi jin daɗi. Kin nunawa su Maami ne?”

Asma’ na murmushi ƙasa-ƙasa cikin murna ta ce, “Ke ni nauyi na ke ji, ba zan iya faɗa masu ba. Ai da kunya ko? Sai na je na ce Maami ga wannan kayan saurayina ya ban, ko me zan ce?”

Murmushi Umm Adiyya ta yi a hankali ta ce, “Ki na sonsa sosai ko?”

A hankali Asma’ ta lumshe idanu, ta sauke numfashi ta ce, “Ban taɓa jin komai ba, kamar yadda na ke ji game da shi, you know, koman shi kyau yake min, kin san ban taɓa gamuwa da wanda ya iya furuci yake kuma natsar min da zuciya ba, kamarsa. Ke ko a wurin aiki, kin ga yadda yake mu’amala da mutane kuwa? He is so nice.”

A take Umm Adiyya ta hau ɓari, idanunta suka fara muntsininta, hawaye suka fara zuba da sauri ta ruga, (Toilet) da gudu, saboda tabbas yadda take ji game da shi, ita ma kenan. Yau ta shiga uku. Adda Asma’ ma tana sonsa kamar yadda shi ma yake sonta.

Asma’ dai sai bin ta, ta yi da kallo lokacin da ta fito daga banɗaki. “Yaya dai Ummu A.? Lafiyan ki kuwa?”

Yaƙe ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta ce, “Babu komai, ciki na ne kawai ya murɗa lokaci guda, ina ga miyar taushen da muka ci da ranar nan ne.”

“Ayya Allah ya sawwaƙa, akwai flagyl ai ba sai ki sha ba?”

“Adda Asma’ ke da shan magungunan nan naki? Na san ma zai tsaya Inshaa Allah.”

“Ke bari, ba a wasa da lafiya, shi ya sa za ki ga abu kaɗan na damu.”

Bargo kawai ta shiga, ta juya mata baya, saboda ita kaɗai ta san me take ji a wannan lokacin. Ita da ace Yaya Zaid wata daban ma yake so da sauƙi, amma Adda Asma’ fa ita ce ‘yar-uwarta da take matuƙar so, ba za ta taɓa iya shiga tsakaninsu ba. Dole ta yakice Yaya Zaid a cikin ranta, ta koya wa kanta rayuwar da babu shi a cikin tsarinta.

Wannan ya sa tun saura sati hutun su ya ƙare, ta gama sayen duk wani abin da za ta buƙata, ta haɗa Jakarta, ta yi masu sallama sai Bauchi.

Karatu kawai take yi haiƙan, koda ta tashi yin IT ɗinta ma, ba ta koma ba, a nan Bauchi ta yi, sai dai ta je Abuja sama-sama, ta ƙara dawowa. Duk wanda ya santa, zai yi wuya ya gano canjin a wuri nata, saboda daman can ba ta da hayaniya, wannan ne ya ƙara ba ta damar ɓoye sirrin zuciyarta.

Ranar Alhamis bayan ta taso daga wurin da take IT ne. Adda Zubaida ta buƙaci ta yi mata rakiya zuwa kasuwa, daga nan suka wuce gidan su Baban Walid, saboda dubo Hajiyarsa.

Daidai ƙofar gidan su Baban Walid ɗin suka haɗu, “Sorry.” Ta faɗa, saboda shige masa gaban hanyar wucewarsa.

“Babu komai, Bismillah.” Ya faɗa cikin wata nagartacciyar murya.

Fitowar Adda Zubaida ne, ya sa ya ƙara faɗaɗa fara’arsa, “A’a babbar Addarmu da kanta, ashe ku ne ku ka shigo?

“Eh, TJ. Ka na nan abinka, sai dai haɗuwar bakin titi.”

Murmushi ya yi, yana wasa da makullin hannunsa, ya ce, “Maman Walid ke dai ki bari kawai, jiya ma na shigo garin. Ina Big Man yake ne?”

“Ai yana cikin gida, ya maƙalewa Hajiya wai yau wurinta zai kwana. Shi ya sa na bar shi. Na ga alamar kawai drawer ɗin shi zan kawo nan, saboda yana so ya ƙauro ƙarfi da yaji.”

“Ah, to ya ga sakewa, ba dole ba, anyway, sai na shigo ko zuwa anjima ko gobe da safe”.

“Goben dai TJ. Na san ka sarai, za ka sa na ajiye maka abinci ka shanyani da abina.”

Tana dariya ta sa Remote ta buɗe motarta. Umm Adiyya ta kama hannun ta buɗe ta shiga, yana murmushi ya mata kallo ɗaya, sannan ya wuce cikin gida.

“Adda Zubaida ke da dangin mijinkin nan kun iya surutu, shi ya sa ba na son rako ki gidansu Baban Walid, idan kun samu hira sai ku manta da mutane.”

“Lah, ai wannan ba komai bane, idan TJ. Ya so surutu, ni karan kaina yana fin ƙarfina, shi ya sa da kansa ma ya ce sai ya sameni a gida ya san kansa. Wannan shi yake bin Gimbiya daga Baban Walid sai ita, sannan TJ. A Lagos yake aiki da NPA (Nigerian ports authority) Ya kan kwana biyu kafin ya zo. Yana da kirki sosai.”

“Hmm! Ke duk dangin mijinki waye bai da kirki? Kowa haka ki ke ce masa mai kirki.”

Dariya ta yi ta ce, “To ba gaskiya bane? Ai yabon gwani, ya zamo dole, kuma ba laifi gaskiya ‘yan-uwan Baban Walid suna so-na kuma kirkin su is natural.”

Haka dai suka yi ta hirar har suka isa gida. Ai kuwa washegari suna zaune a falo sai ga TJ. Ya shigo. Gaisuwa kawai ta haɗa su da Umm Aɗiyya, ta miƙe za ta bar falon, ruwa ta kawo masa da drinks, sai abinci, tunda Adda Zubaida ta riga ta shirya.

Tana ajiyewa ta wuce ciki, daman zaman nata ma Baban Walid ne yake mata tsiya, wai sai ta kunsu a ɗaki kamar kayan wanki, shi ya sa take fitowa, to idan sun yi baƙi kam ɗakin Adda Zubaida take zamanta.

Tana wucewa TJ. Ya ɗebi  juice ɗin da suka yi da carrot da ginger ya sha, sai ya ce, “Maman Walid baƙuwa ku ka yi ne?”

Dariya ta yi ta ce, “Amma dai TJ. Akwai ka da tsiya. Umm A. ɗin ce ba ka gane ba ko me?”

“No, seriously, wannan ɗin Umm Aɗiyya ce?” Ya tambaya cikin ɗaga gira.

“Shi ya sa mana, na ga ka na wani kama kai, ka ɗauka wata ce, ka ɗan latsa ko?”

Cikin murmushi ya shiga sosa kansa, “To ai, Maman Walid ya zamo dole a yi wani abin akai, don gaskiya har ga Allah tun jiya da ku ka wuce, yarinyar ta tsaya min a rai, ashe ma ta gida ce, shi kenan, ai ni kam ta faɗo min gasasshiya.”

Tana dariyarsa ta ce, “Wannan jan aikin kam na bar maka. Ummu A. Lamarinta sai ita. Ka sameta ku yi magana, wannan kam ba ruwana a ciki.”

“Haba dai kuma babbar Adda, kar mu yi haka da ke mana, an ce fa babbar Ya, uwa, ba za dai ki so ki bar ni cikin matsala ba ko? Ki ɗan shige min gaba ko yaya ki ka ce?”

Zaro idanu ta yi ta ce, “Wuuu! Wannan ɗin? Ga dai lambarta karɓa, ka nemeta, idan ku ka daidaita, sai na yi maka kamfen.”

“To an yi, an gama, tunda kin bada goyon baya. Yaya kam bai shigo ba, har yanzu ko?”

“Ya kusa, na san yana ma hanya yanzu kam.”

“Ni ina ga zan wuce, ki gaishe shi, za mu haɗu gobe Inshaa Allah.”

“Ba ga irinta ba, ai yau babu inda za ka je, sai ka cinye abincin nan tas!”

Yana dariya suka ji sallamar Baban Walid, “Yawwa shi kenan, ga shi ma ya dawo sai ka zauna da tushe.” ƙarasawa ta yi zuwa wurin mijinta, ta yi masa sannu da zuwa, ta karɓi kayan hannunsa zuwa ciki. Sai da ta tabbatar ya samu natsuwa, sannan ta bar su a falon ta yi ciki.

**********

“To sarkin tunani, an fara aikin ko?”

“Adda Zubaida da ba ki bar Walid ba, gidan ya yi shiru da yawa.” “Ai ya je can dai ya ɗanɗana masu, ni ma ko zan ɗan samu hutu.”

Murmushi ta yi ta ɗauki wayarta tana kallon hotuna, can kuma ta ajiye ta shige wanka, koda ta fito Adda Zubaida ta shiga, don haka ita ma ta yi shirin barci, ta kwanta. Baƙuwar lambar da ta gani a wayarta ce, ta sa ta ɗaga wayar tana ganin fuskar da kyau. Kamar ba za ta ɗaga ba. Can kuma da aka sake kira, sai ta ɗaga don ta ji wanene.

“Assalamu-Alaikum.”

“Wa’alaikis-Salam, kin wuni lafiya?” Ya faɗa, bayan shiru ya ɗan ratsa maganar da ta yi.

Muryar da ta ji ne ya sa ta shiga tunanin inda ta taɓa jin muryar, amma ta manta. Kafin ta tambayi ko wayene, ta ji an ce, “Ki na magana ne da Tijjani Muhammad Gital. TJ. Da fatan ban katse miki barcin ki ba.”

Idanu ta fitar waje kawai, numfashinta yana neman ya gagareta.

Da ƙyar ta samu numfashinta ya dawo daidai. Ko ba ta tambaya ba, ta gane yanzu kam, TJ. Ne ƙanin Baban Walid.

“A’a ina dai shirin yi.”

“To dama na kira ne mu gaisa, amma tunda za ki kwanta, bari na bar ki, sai da safe ko?”

“Ba komai, wani abu ne?”

Tambayarta ta so ta ba shi dariya, amma ya ce, “Idan har ba kya sauri, za ki iya jin koma menene zuwa gobe da yamma, idan you are free.”

Ta san ba yadda za ta yi masa ƙarya ta ce tana wurin aiki, saboda washegari Asabar ne. Don haka ta ce, “To Allah ya kai mu.”

“Na bar ki lafiya.” Kawai ya faɗa, ya kashe wayar. Duban nata kan wayar ta yi ta haɗe rai, ta san ba mai wannan aikin, sai Adda Zubaida!

***************

BABI NA HUƊU

“Adda Zubaida ke ma kin san ba ki kyauta min ba kwata-kwata, yaya ma za ayi ki fara ba shi lambata? Wallahi darajar Baban Walid ya hana na surfa masa mai zafi, me ya sa zai karɓi lambata a wani wuri, bai nemi izini na ba?”

Adda Zubaida ta ɓata rai ta ce, “Ni ɗin ce wata? Ni ban san meye matsalarki ba, ke ba dama wani ya tunkareki da magana kamar wata ‘yar Secondary school. Shi kenan ki hau fada? Tabbata za ki yi a haka? Sai Abba ya miki auren sadaka, za ki sani ai, don kowa ya gaji da saka miki idanu. Ina laifi ki ɗan ba shi dama ki ga yadda za ku ƙare?”

Turo bakinta ta yi gaba ta ce, “Ni Adda Zubaida, gaskiya ba yanzu zan yi aure ba.”

“Yanzu shekarunki ashirin da biyu, sai kin yi talatin ne za ki yi auren ko kuwa me ki ke jira? Bari na faɗa miki, idan mace tana cikin lokacinta ba ta natsu ta kama dahir ba, to na faɗa miki gaba kaɗan, sai ta rasa me zuwa ko tayawa ne, ke kin fi ni sanin wannan.”

A ranta ta ce, “Ni kam ban san meye bane a cikin rabona ba, amma na san ba zan taɓa son kowa ba bayan Yaya Zaid, shi kuwa ya wuce inda na ke, don haka aure kam sai dai randa Allah ya ƙaddaro ko ma da waye ne, shi kenan, amma ba ni da lokacin wata soyayya.” Hawaye ne suka fara bin fuskarta, don haka ta miƙe ta wuce ɗaki.

Adda Zubaida kam bakinta ta riƙe tana ganin ikon Allah. Haka suka zauna kwanaki biyu ba ta shiga sabgarta, wai a dole tana fushi. “To wai har yanzu ba ki huce bane? Ina ce kin faɗa masa ba ki shirya ba, shi kenan shi ma Allah ya haɗa shi da rabonsa.”

“Adda Zubaida, ba wai na ji haushin turo min shi da ki ka yi bane, amma ke ma kin san Abba yana samun labarin ƙanin Baban Walid ne, ko ba mu daidaita ba, shi kam zai yi na’am, don yadda ki ke yabonsu, haka kullum shi ma yake yabon jama’ar gidan.”

“To meye ne a ciki? Bayan ke ma kin san cewa yana da halin ƙwarai, kuma bai da makusa. Kowa matarsa yake aura, idan ba ki cikin rabonsa, ba yadda za ayi komai ya ɗaure, kawai lokaci za ki ɗan ba shi, shi kenan fa!

Hannu ta harɗe a ƙirji tana gunaguni. “To shi kenan na ji, amma kar ya kuskura ya nemeni a Abuja, don ba na son Abba ya gan shi. Bare ma magana ta yi nisa.”

“Ummu A. Ko dai akwai wanda ki ke so ne?” Jin tambayar Adda Zubaida ya sa sai da ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, nan da nan ta hau kame-kame da inda-inda.

“Ah, Adda Zubaida so kuma? Ai tare muke zaune, da akwai wani, ki na ga da ba ki sani ba?”

“To ai na ga yadda ki ke kafewa ne akan rashin son kula kowa, abin yana damuna.”

“Kar ki damu, ba komai, our able Maman Walid.” Ta faɗa tana murmushi haɗe da rungumo ‘yar-uwarta, hawaye ne ya biyo fuskarta, ta yi saurin share su, sannan ta ɗago tana yaƙe.

Adda Zubaida na fita daga ɗakin ta kwanta kan filo ta shiga risgar kuka kamar an aikota. Ita ta rasa wannan wace irin jarabawa ce. Wai ace duk tulin waɗanda suke cewa suna sonta, ta rasa wanda za ta so a cikinsu, sai wanda bai san ma tana yi ba? Bayan hakan ma, ya yi nisa a wurin ƙaunar ‘yar-uwarta.

***********

TJ ko bai saduda ba, duk da wasu lokutan ya kan ga kamar ba haske a al’amarin. Musamman da yake Lagos tana Bauchi, amma hakan bai sa ya karaya ba, kullum yana cikin mata waya.

Wataran su shirya, wataran a baɓe, duk randa zai mata magana kan abinda yake ji game da ita, to faɗa za su yi kaca-kaca, idan zai kawo mata wata hirar ta ɓangaren ilimi, to nan ne za su shirya.

Hutu ne kawai ke kai ta Abuja, don wataran ko bikin sallah a Bauchi take kayanta. Komawarsu final year ne, ya sa ta ji tamkar da wasan yara take yi a karatun, don haka ta maida hankali kacokam ga karatun ta. Ta kwantar da hankalinta har wani ɓulɓul ta yi. Kwatsam! Ranar Asabar Asma’ take shaida mata za a zo ayi tambayarta.

“Ke yau ba wanda ya kai Dee murna, kamar an ce yau ne ɗaurin auren. Ummu A. Ki tayani addu’a.”

Wani ƙarar murna ta saka ta ce, “Hinyau su Adda Asma’ amare, don Allah kar su ce za ayi auren a wannan shekarar, ku jira sai na gama ina gida.”

“Ka ji ki dai, sai mu yi ta zaman jiranki, randa A.T.B.U ɗinku suka ga daman shiga yajin aikinsu kuma fa? Lalle ma lokaci kawai za ki samu ki taho.”

“To Allah dai ya tabbatar da alkhairi.”

“Ameen. Kar ki damu, zan ce Maami ta bar sauran Shopping, sai kin zo sai mu yi tare.”

Cikin ƙarfin hali Umm Adiyya ta ce, “To shi kenan, Allah ya kai mu.”

Murmushin tausayin kanta kawai ta yi, sannan ta ɗaga littafin (Micro Computer & Micro Electronics) ɗinta tana dubawa, sai dai maimakon ta fahimci abin da take karantawa, sai ta ga komai ya dawo tamkar zare.

Sai da ta dage da addu’a, ta samu natsuwarta, ta mance da komai. Suna tare da su Idris ne, bayan sun taso daga wani gwajin da suka yi, suka ga ta tsaya cak! Hannayenta rungume da handouts ɗinta da wayarta.

“Umm Adiyya lafiya?” Muhammad ya tambaya. A hankali ya ɗago ya dubi inda idanunta suke kallo. Ganin mutumin yana masu murmushi, ya sa ya saki ajiyar zuciya.

“Ba ki san shi bane?”

Yaƙe ta yi ta ce, “Yayana ne.” Ta faɗa tana kallon Zaid da ke tsaye sanye cikin v-neck shirt da jeans da agogon silver na chain da ya kawata hannunsa.

Nan da nan ta seta tunaninta, saboda kar ma ya gane komai, ta ƙarasa inda yake tsaye jikin motarsa, a wurin Parking ɗin motoci a gaban Complex.

“Yaya Zaid yaya aka yi ka san inda za ka sameni?”

Murmushi ya yi, bai ba ta amsa ba, sai da ya miƙawa su Idris hannu, waɗanda suka fara gaishe shi. “Ina wuni Yallaɓai?”

“Assalamu-Alaikum, yaya karatun dai ana ta fama?” Ya faɗa fuska a sake.

“Eh, Wallahi.” Muhammad ya ce.

“To ya yi kyau. Allah ya taimaka.”

“Ameen-Ameen.” Dukansu suka amsa.

Sai da suka wuce ne, ya bi su da kallo ya dubi Umm Aɗiyya, “Ke kuma ‘yan maza ne ƙawayenki?”

Ya so ya ba ta dariya, amma yanayin da ta ke ciki ya hanata wannan daman. “Test muka fito.”

“Muna tare da Saadiƙ ne, amma ya tsaya can wai za su gaisa da wata Saudat ce ko waye?” Ajiyar zuciya ta yi, shi ya sa mana Saudat ta isheta da tambayar labarin ‘yan gidansu, wato daman Yaya Saadiƙ ne ya ɗan zagayo.

Cikin ƙarfin hali ta ce, “Yaya hanya?”

“Lafiya ƙalau. Mu ƙarasa ko ba hostel za ki koma ba?”

Ba tare da ta amsa ba, ta zagaya ta zauna a ɗaya gefen. Yana shigowa ta ce. “Congratulations.”

Juyowa ya yi ya kalleta, sannan ya ƙarasa saka seat belt ɗinsa “Na gode duk da ban san na meye bane wannan.”

Ta gefen idonta ta dube shi, idan ma ya zo ne ya ƙara juya mata tunani ko lissafi ba za ta taɓa barin hakan su faru da ita ba, don ta gama da wannan ɓangaren na rayuwarta.

A hankali suke tafe, har suka ƙarasa (NANA KHADIJA HOSTEL). Nan suka gaisa da Yaya Saadiƙ, ita dai Allah-Allah ma take yi su tafi, a wani ɓangaren don ta gamu da Saudat, a ɗaya ɓangaren kuma ba ta son ko ganin Yaya Zaid.

Cikin ikon Allah, bai wuce minti goma ba, suka ce za su wuce don suna kan hanya, saboda Yaya Saadiƙ zai koma Gombe ne, yayin da Yaya Zaid kuwa wani aikin ne ya kawo su Bauchi. Don haka suna tafiya ta sauke numfashi.

Bayan sun koma ɗaki ne ta dubi Saudat ta ce, “Asirinki ke ma ya tonu, wato daman abin kenan, shi ne ki na ƙus abinki. To Dangin miji mode activated, bari na faɗa miki, zan zuga shi ya fasa, tunda ba a ban kula na musamman ina matsayin ƙanwar miji guda.”

Saudat na dariya ta ce, “Ai yayankin nan abin tsoro ne, don haka na bar maku kayanku, ke daga zuwa sau biyu, yana min maganar zuwa gida. Haka daman ‘yan Nafaɗan nan ku ke ne?”

“Ke kin samu an bi ta kanki ma? Kar ki mana yanga, dama ki bada go ahead, ehem.” Ta faɗa, ta na zaro mata idanu. Su Taƙiyya suka sa masu dariya.

**************

Yau ga shi watanni biyu da gama Service ɗinta inda ta yi a Jigawa State, dole ta sa ta koma gida gaba ɗaya. Banda TJ. Babu wanda take bawa fuska, shi ɗin ma kullum sai ya sha fama take saurarensa. Shekarar su kusan uku tare, amma kullum idan yana son zaman lafiya, to kar ya ɗago mata maganar aure.

Wannan ya sa ya ɗaga mata ƙafa. “Ina ga Umm Aɗiyya, ki na buƙatar lokaci, ki yi nazarin abin da yake tsakanin mu. Kin ga dama ba kusa muke da juna ba, so zai fi kyau ki fuskanci me ki ke so ɗaya, duk abinda ki ka yanke nan da watanni biyu, ina saurarenki.”Ita kanta ta san ta ƙure TJ. Amma ta tabbata ba don ta wurin Adda Zubaida ya fito ba, da bai samu hakan ba ma.

************

Tana karanta wani magazine ne, suka shigo falon suna dariya, “Yanzu da gaske ba za ka zaɓa ba?”

“Ni kuma me na sani kan wannan? Yawwa ga Ummu nan ta taya ki.”

Asma’ tana murmushi ta isa inda take zaune ta hau buɗe mata catalog. “Ummu A. kin ga Yaya Zaid ya ki ya tayani zaɓa, wanne ki ka ga ya fi dacewa?”

Fiddo idanu ta yi cikin razana, tana duban su dukan su biyu. Tashin hankali! Yanzu haka za ta zauna a gidan nan tana ganin abin da ya fi ƙarfinta? Yaya za ta fara zaɓa masu kujerun da za su yi amfani da shi a gidansu?

Murmushi kawai ta yi ta ce, “Adda Asma’ ku da gidanku, ai za ku fi ni sanin me zai dace da gidan da wanda ranku ya fi so, duk da dai wannan gray ɗin ya yi kyau sosai.”

Ta fada haɗe da rufe littafin hannunta, ta miƙe daga falon. Asma’u ta dubi Zaid, ta samu shi ma kallonta yake yi, ta ɗaga masa hannaye alamun ba ta san amsar ba ita ma.

Tun da ta shige kuwa, take aikin kuka, a nan ta yi zamanta har sallar Issha, sai da Abba ya kirata, sannan ta fita ta ci abinci, ce masu ta yi idanunta ke ciwo.

“Na ga alama kin zama sauran Likita, za mu kai ki asibiti mu bar ki a can ko ba haka ba Mamana?” Abba ya faɗa cikin zolaya.

“Fa’iz ga wannan ka samo mata eye drop, mai kyau ko idon zai wartsake.” Abba ya faɗa.

 

Fa’iz yana jin ya cika saurayi har saurayi, ya sosa kai ya ce, “Ah, Abba bar shi kawai akwai kuɗi a jiki na.”

Faruƙ ne ya ce, “Da kyau, Don! Ni ma ka sayo min iPhone charger, nawa ya ƙone.” Harararsa ya yi ya ce, “Don Allah gafara Malam, Maami ki sa Faruƙ a hanya. Wallahi son banzan shi ya fiye yawa.”

Dariya suka yi kawai, don muddin suka haɗu wuri guda, to ba za ka ji kunnenka shiru ba, tsabar faɗa, amma fa ba a taɓa ɗayansu a share. Kafin gari ya waye kuwa Asma’ ta tsinci Ummu Aɗiyya cikin zazzaɓi mai zafi.

************

A ƙudundune take a lungun gado, kan sallayah, banda kakkarwa, babu abinda take yi, ba ko tantama ta san zazzaɓi ne ya saukar mata, sai dai ko hoɓɓasan neman magani Umm Aɗiyya ba ta yi ba, don ta san ciwonta bai da magani. Sai dai sauƙi kawai daga wurin Ubangiji, wanda yanzu haka ta gama kai kukanta ne, zafin zazzaɓi ya hana mata tsayuwar sallan daren ma da ta tashi, domin yi, shi ya sa ta koma yin tasbihi.

Jin shessheƙar kukanta ne ya sa ‘yar-uwarta Asma’ ta farka daga barci, ta kunna wutar ɗakin, saboda daga ji kukan ba na lafiya bane. “Ummu A? Me ya sameki ki ke kuka haka?” Ta faɗa daidai lokacin da ta durƙusa a gefenta tana shafa kanta, saboda yadda ta ga tana kakkarwa.

A hankali ta buɗe idanunta, wanɗada suka yi jazur! Kamar jan gauta, ga kuma azabar ciwon kan da hasken ɗakin ya ƙara mata. “Babu… Ki kwanta Adda Asma’u.”

“Yaya za ki ce min babu? Kin ga yadda ki ka koma kuwa, bari na samo miki magani ki sha. Zazzaɓi fa ki ke yi mai zafi. Amma kamar farilla, sai kin yi wannan tashin daren naki, ki huta mana, don na yau kawai, ai jiki ma yana da haƙƙi kan Ɗan- Adam.”

Da sauri ta miƙe ta nufi durowar jikin madubi, ta fito da robar adana magunguna (first aid box). Panadol Advance ta ɓalla ta ba ta, ta miƙa mata kofin ruwa.

“Karɓa ki sha, don Allah Ummu A. Ki sa wa kanki sa’ida, haka nan, na kula kin fi sati biyu a wannan halin da ki ke ciki na damuwa, kuma na san shi ya sanya miki zazzaɓi. To ki sani idan ba ki daina damuwa ba, zan faɗawa su Maami halin da ki ke ciki, kuma kin san taron dangi za ayi a kanki, sai kin faɗi matsalarki. Ko ba ki faɗa min ba, ki daure ki cire damuwar a ranki, ki barwa Allah komai kin ji?”

Murmushi ta yi na ƙarfin hali da kuma yaba yadda ‘yar-uwarta take matuƙar ƙaunarta. “Adda Asma’ ni ba ni da wata damuwa, kawai dai jikin nawa ne ya ƙi daɗi. shi ya sa. Amma tunda na sha magani. Inshaa Allah shi kenan.”

Asma’u ta zura mata idanu, tamkar tana so ta karanto ƙaryar da ta sharara mata. Don dukkansu sun san juna ciki da bai, yadda ba yadda za ayi ɗaya na cikin wani hali ɗaya bai sani ba. Hakan ne ma ya sa Umm Aɗiyya ta san cewa lallai ta iya zurfin ciki, tunda ko ‘yar-uwarta ta kasa gane yaudarar da zuciyarta take son tay5i mata na cin amanar ƙaunar da ke tsakaninsu.

Eh, mana lallai zuciyarta ta yanko mata wani ɗanyen aiki ja, wanda ba ko tantama zai jefa ta a halaka ne kawai, ya kuma raba dangantakarta da ‘yar-uwarta, wannan ya sa ta gwammace ta zauna, koda ciwo zai kasheta ne, gara ya kashe, amma ba za ta bawa zuciyarta abinda take so ba. Domin abinda take so haramtacce ne a gareta.

Lokacin ne ta ƙara haɗiye hawayenta, ta kuma sa hannu ta goge fuskarta, haɗe da miƙewa cikin jiri-jiri, ta isa banɗaki, domin wanko fuskarta. Saboda yanzu kam ta yanke wa kanta shawara, komai zai faru da ita, sai dai ya faru, amma ko shi ne autan maza, wajibi ta haƙura da shi. Ba za ta taɓa yarda soyayyarsa ta raba tsakanin su ba.

************

2010 RANA TA YAU.

 

Tana riƙe da wayarta tana karanta wani shafi a yanar gizo ne a falon Abba ta ji alamar shigowar mutum, wannan ya sa ta ɗaga idanu ta dubi mai shigowar, sallamarsa ce ya sa ta yi saurin miƙewa a zabure da nufin barin falon, sai kuma ta tattara natsuwarta ta daure ta gaishe shi.

“Yauwa lafiya Ummu, yaya Maami, tana kusa ne ki mata magana?”

Murya a sarƙafe ta ce, “Eh… Bari na faɗa mata.”

Gabaki ɗaya haibarsa ruɗata yake yi, yana da wani abu a tare da shi wanda muddin yana wurin, dole ka ji a jikinka, ga wata natsuwa ta musamman da hatta kalamansa a natse suke fita. Idanunsa kuma…. Kafin ta ida fasalta shi a zuciyarta, ta shiga firgici, a dalilin ji da ta yi ya ce.

“Ummu.” Ya kira sunanta a cikin dakewa kamar yadda ya saba, tana juyowa ya ce, “Ki taho min da ruwan sanyi.” A hankali ta gyaɗa masa kai ta wuce cikin gida, na daƙiƙa ɗaya ta mayar wani abin zai faɗa mata wanda take matuƙar son ji daga gare shi, sai dai wannan kam sai dai a mafarki, domin ita ba komai bace a gare shi, face ƙanwarsa da kuma ƙanwar matar da zai aura!

Hannunta na rawa, duk da faɗan da ta yi wa kanta tana nanatawa cewa babu ruwanta da shi. Babu ke, babu shi, babu abinda zai shiga tsakaninku, ba ki san shi ba baicin shi yayanki ne kawai. Amma wannan bai hana hannunta rawa ba, a yayin da take zuba masa ruwan sanyinsa.

“Ummu, lafiyarki ƙalau kuwa?” Ya tambaya saboda shi kansa ya santa da natsuwa, amma sai zuba ruwa take yi, yana zuba ba tare da ta sani ba.

Shigowar Justice Khadija falon ne, ya sa duka hankulansu ya koma kanta, tana murmushi ta ce. “Hmm! Kai ma dai Zaid ka tambayeta, haka nan ta rikiɗe mana mun kasa gane kanta.”

Asma’ ce ta shigo ta ƙofar da Zaid ya biyo, wanda hakan ba sabon abu bane, domin a office ɗinsu take aiki, mafiya lokuta tare suke zuwa aikin ma su dawo tare. “Kun sa min ‘yar-uwa a gaba, zazzaɓi ta kwana da shi, shi ya sa amma da sauƙi.”

Zaid ya ɗauki glass ɗin ruwan ya zauna, sannan ya ce, “Sweetheart, Yaya za ki ce da sauƙi, bayan hannunta rawa yake yi da take zuba min ruwa?” Ya faɗa idanunsa a kafe kan Umm Aɗiyya, wannan ya sa ta kasa tsayuwa a wurin, ta wuce ciki da sauri, zuciyarta na bada wani ɓalli-ɓalli tsabar kishin yadda ya kira ‘yar-uwarta. Domin ba abinda kunnuwanta suke rattabo mata illa kiran Asma’u, sweetheart da yake yi.

“Maami ki dai bincike ta sosai, akwai wani abin, ko kuwa ku kai ta asibiti.”

“Rabu da Ummu da shirmenta. Banda abin ta yaya tana zazzaɓi sai ta yi shiru? Ciwon bai ci ta bane, shi ya sa. Ta ce ka na nemana.”

Ajiyar zuciya ya yi, sannan ya ce, “Yawwa Maami, daman shawara na ke so mu yi.”

Murmushi ta yi ta zauna, sannan ta ce, “Ina jinka.”

 

Haka nan zuciyarta cike fal! Da daɗi, saboda yadda Zaid ya ɗaukesu daga ita har mijinta tamkar su suka haife shi, sam baya wani ja da baya ko ya nuna shi ba ɗan gidan bane a kodayaushe, kai tsaye yake samunsu da matsalolinsa, ko shawarwari, ko yanzu ma kan maganar auren Asma’, shi ne kan gaba a komai.

Asma’ kam wuri ta ba su da ta ji za su yi shawara, can ɗaki ta koma ta samu ‘yar-uwarta, sai dai duk labarin da take mata, banda uhm da uhm-uhm, ba abinda take cewa koman shiru shirunta dai, wasu lokutan ta kan tanka. Musamman yau da ta ba ta labari mai ban dariya, ta kula ko murmushi ba ta yi ba.

“Haba Ummu A, tun ɗazu kin maida ni kamar mahaukaciya, sai surutu na ke yi ni kadai? Ke Wallahi ba ki da daɗin yin hira sam!”

“Na yi magana da Adda Zubaida, Energy Commission sun neme mu Intabiyu, ran Asabar zan tafi Inshaa Allah, don litinin ne Intabiyu ɗin.” Ta faɗa cikin kawar da ƙorafin ‘yar-uwarta.

Da gudu Asma’ ta rungumota tamkar ta ce mata aikin ta samu. “Kai nayi miki murna ƙwarai. Allah ya ba ku sa’a, ya sa a dace, hinyau za ki zama ‘yar Bauchi kenan.”

“Adda Asma’ ba ki ga dai na samu ba tukun.”

“Are you kidding me? (Ki na wasa dai), ta yaya za ki faɗi wannan Interview ɗin? ƙanwata mai nasara ce kuma za ki ci Inshaa Allah.”

Murmushi ta yi kawai, domin ba komai ya sa ta zaɓi ta nemi aikin ba tun farko, illa saboda ta gujewa Yaya Zaid, domin muddin tana ganin sa zuciyarta ba za ta bar ta ba, son shi ba zai bar ta ba.

Amma idan ta yi nesa da shi, ta san dole ta yi haƙuri ta mance da shi. Shiru ta yi kawai ta shiga tunanin tun farko me ya jefata cikin wannan abu mai wuyan fitan?

**************

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *