Halin Girma – Tsakure

FRANKFURT, JAMUS

24 YULI, 2010 — 7:31 PM

 

“Sannunku, Fasinjoji daga jirgi na 17 zuwa Tel Aviv, an canza ƙofar tashi zuwa ƙofa ta 16A. Za a samu jinkirin tashi, saboda mummunar yanayin waje. Ƙungiyar da ke ƙasa na kan aikin cire ƙanƙara daga fuka-fukan jirgin, domin shirin tashi .

Har ila yau kuma jirgin cike yake da mutane. Don haka muna miƙa kyautar tikitin zagayen tafiya da dawowa zuwa ‘Yan fasinjojin da a shirye suke da su bi jirgin baya.

Za mu fara bodin nan da minti arba’in. Mun gode da haƙurinku.” Matar da take magana daga muryar komfuta, ta gama jerowa cikin shiryayyen turancinta, kafin ta sake rattaɓowa cikin wasu fitattun yarukan duniya masu dama. Ƙwarai ba haka fasinjojin suka so ba, kasancewar sun riga sun yi kusan awa guda suna jiran a kirasu.

************

MASDOOK

Ya ilaahi. Yanzu mutum sai ya sake jiran kusan minti arba’in a wannan wurin? Allah dai ya sa kar na makara, domin kuwa ba zan iya jure babban asarar da za mu yi ba, muddin ban isa a kan lokaci na haɗu da Adir ba.

Ganin jiran ba na lokaci ƙalilan bane, ya sa ya shiga neman wurin da zai ɗan rage aikinsa, can ya hango wurin zama. Don baya son zama cikin falon baƙi na musamman, hakan ya sa ya fito wurin jira na jama’a baki ɗaya, ba tare da ya shiga wurin hutawar baƙi na musamman ɗin ba.

**********

MIHJANA

Littafin hannunta ta rufe, duk da ba ta son waiwayawa ta ga abin da yake faruwa, hatsaniyar ta dameta, agogonta ta ƙara kallo a karo na uku. Ba ta san lokacin da za su tashi ba. Yanzu ma an jinkirta tashin jirginsu, dalilin da ya sa take zaune a nan kenan a karo na farko, sakamakon rasa jirgin da ya dace ta shiga da ta yi. Bayan sun tsaya, domin shiga jirgin da zai ƙarasa da su Birnin na Tel Aviv.

Ba abinda ta tsana, irin wuni a filin jirgi, duk da dai ba kullum take tafiya a jirgi ba, amma iya tafiyar da ta yi, ta san cewa akwai kularwa da ban haushi, ka zauna tsawon awa uku ko ma fi ka na jiran jirgin da za ku yi tafiyar da ba ta wuci ta awa guda ba, duk da dai yau tafiyar ta su ta kusan awa huɗu ce.

Madubin idanunta ta sake gyarawa da zimmar ci-gaba da duba littafinta. Ihun da ta jiyo alamar hatsaniyar tana ƙara ƙamari ne, ya sa ta sake maida hankalinta garesu. Me ya sa ba ta yi mamaki ba, da ta ga mutumin da ake rikici da shi?

A fadin filin jirgin kaf! A rasa wanda zai kawo irin wannan tashin hankalin, duk gamayyar jama’a na launin fatar bil’adama a wurin, sai dan ƘASARTA? Duk da ba ta da tabbacin ko shi ɗan wace ƙasa ce, ta ga lallai baƙar fata ne, sannan kuma daga jin turancinsa, ɗan ƙasarta ne, ga shi sai ɗaga murya yake yi. Can dai masu kula da harkar tsaro suka yi gaba da shi.

Mihjana ta girgiza kanta cikin takaici da Allah wadaran irin ɗabi’armu da ba za mu iya yin abu mai sauƙi ba, kamar bin dokar wuri koda kuwa wurin baƙo ne a garemu.

Juyowar da za ta yi ne, ta ji tamkar an nausheta a ƙirji don faɗuwar gaba a dalilin razanar da ta yi, domin ko kaɗan ba ta yi tsammanin ganin mutum a zaune a gefenta ba.

Koda wasa bai nuna alamar ya san da mutum a gefensa ba, balle kuma ya yi bayanin zai zauna, to ma haka kawai, idan banda ɗabi’a ta wasu mutane, sai ka kama ka zauna a gefen matar da ba ka sani ba? Duk faɗin wurin nan?

Sai kuma lokacin ta juya ta ga ko ina a cunkushe yake, kasancewar an soke tashin jirage kusan biyar manya-manya.

Daidai nan idanunta suka sauka kan fuskar mutumin da ya ɗauke mata kaɗaiɗantakar  da ta samu, gefe da hatsaniyar wurin. Gabanta ne ta ji ya faɗi, nan da nan numfashinta ya fara fita da sauri-sauri. “Inna-Lillahi’wa-Inna-Ilaihir-Raji’un!” Ta numfasa a hankali.

Cikin hanzari ta juya daga kallonsa, in da gaba ki ɗaya hankalinsa ya yi gaba wurin latsa na’urar komfutar da ke kan cinyarsa.

Kamar daga sama, ta ga wata ma’aikaciya ta tunkare su, kai tsaye wurin mutumin nan ta tsaya, cikin rankwafawa nuna alamar girmamawa tana tambayarsa “Yallaɓai akwai abin da ka ke buƙata?” Cikin harsen turanci ta yi masa maganar, duk da Jamusanci ya riƙa a harshen nata.

Mihjana dai tana kallon ikon Allah, to ita me ya sa ba a tambaye ta ba, ai da ta faɗa masu, don wata fitinaniyar yunwa take ji, ita kuma ta gaji da cin kayan zaƙi da na gishiri, wanda ba zai ɗumama mata ciki ba.

Sai ga shi ga mamakinta mutumin da ta ji an kira shi da Mr. Abubakar, ya ci-gaba da abin da ke gabansa, ba tare da ya bar abin da yake yi ba. Ya-ce “Babu.”

A take Mihjaana ta ce, wannan wane irin mutum ne da kwata-kwata baya murmushi, dubi yadda matar nan ta taso duk ɗimbin jama’ar wurin, ta zaɓe shi, shi kaɗai don ta tambaye shi buƙatarsa, amma ko kallo ba ta ishe shi ba.

To me ya dameni da shi ma?

Ita yanzu babban damuwarta, jirginsu ya zama a shirye, ko za ta bar wannan wurin ta samu ta je ta sauke damuwar da ke gabanta. Musamman ma na abinci, don cikinta har wani ƙugi yake yi.

***********

Masdook ya dubi littafin da ke kan ƙafafunta ta gefen idanunsa, ‘Straight Talk, No chaser’ ya girgiza kai. Ya kan rasa me ya sa wasu mutanen ba su da abin yi kwata-kwata, yanzu wannan littafin me zai amfaneta da shi?

Yana da zimmar ci-gaba da aikin da ke gabansa, amma ya gaza yin hakan, saboda halin da yake ciki, muryar matar da ta fito ta hanyoyin sanarwa ne, ya fiddo shi daga nazarin littafin ƙafafun yarinyar hakan ya ɗauke shi, bazata har wayarsa ta faɗi a gefen ƙafafunta, garin ya sunkuya ya ɗauka ne, kansa ya bugi goshin Mihjana da ta yunƙura domin ta tashi.

“Oucchhh!” Ta faɗa cikin girgiza wurin da ta buge, shi ko tamkar bai bugu ba, ɗagowa ya yi cikin hanzari, ya gyara madubin idanunsa, na ƙara ƙarfin gani, sannan ya ce “Sannu.”

Kallonsa ta yi cikin tsananin mamakin kalmar da ya faɗa “Sannu?”

Ɗaga girarsa ya yi sama yana duban gefensa da bayansa, sannan ya sake dubanta “Ko kuwa ba abinda ake faɗa ba kenan, idan mutum ya yi laifi cikin kuskure?”

“Kuskure?”

Kallonta ya yi wani iri, lafiyar wannan? Kodai ita ce ba ta iya magana ba, sai tambayoyi ta iya? “Ka zo ka sameni a wurin da na ke zaune ni kaɗai, ka zauna a gefena ba tare da neman izini ba, ka wurgar min da waya, ka fasa min ita, ka buge min kai, iya kalmar da za ta fito a bakin ka kenan? Sannu?”

Shiru ya yi yana duban ‘yar mitsilar yarinyar da take masa magana. Daga bisani ya kalli wayar hannunsa, sai ya ga ashe ba tasa bace, ga tasa a aljihun jakar kwamfutar tafi-da-gidankansa . “Okay, na yi kuskure, ki yi haƙuri, shi kenan ko?”

“Ban san wanda ya koya maka bada haƙuri ba, amma koma waye ne, na tausaya masa ƙwarai, domin yana da sauran aiki a gabansa.”

Ta faɗa a tsume haɗe da ƙwace wayarta daga hannunsa. Masdook ya bi ta da kallo, bai taɓa ganin yarinya kamar wannan ba, wacce ta tsaya ta fuskance shi ta faɗa masa magana son ranta ba, duk da ya san laifin sa ne.

Amma kuma ita waye za ta faɗa masa son ranta, mata kamarta nawa suke Allah-Allah ya dubi inda suke. Ita ta samu ma har ya yi mata magana, har tana kushe wanda ya koya masa tarbiyya! A lokacin ji ya yi kamar ya fincikota ya tsinke bakinta, gobe ba za ta ƙara yi wa wani tsiwa ba.

Ta fara tafiya ne, ta ji kamar an taɓa ta, amma ta juyo ba ta ga kowa ba, tsaki ta ja ta ci-gaba da tafiya. Haka kawai tana ji da wayarta, ya kama ya zo ya fasa mata waya. Ita ba ta taɓa ganin mutum irinsa ba.

Yaya ma aka yi ya iya Hausa, oho? Don ita kallon Masdook tun farko ma ba ta ba shi ɗan Najeriya bane, balle ta sa shi a kabilar Hausawa, don tamkar Balarabe haka komansa yake, ga shi jibgege, duk tsawonta sai da ta dawo mitsitsiya a gabansa, tana masa masifa ma, tana tunanin idan ya mutsuketa, sai dai a sake wata Mihjanan, ba ita ba. Ganin yana da siffar larabawa, ya sa ta yi saurin danganta shi da Musulunci.

Shi ya sa ta yi ta jin haushi da ya kama gefen kujerarta ya zauna, ba tare da ya tambayi koda me wurin ba? Watau in babu ya nemin izinin ko zai iya zama, kasancewar dai da hijabin ta ya ganta a jikinta.

Duk da yake dai ƙaramin hijabi ne, amma ai rigarta me dogon hannu ne. Ta faɗa a ranta haɗe da duban kayan jikinta. Doguwar rigar Turkiyya ruwan ƙasa mai cizawa da kuma ɗan hijabin ta da ya shiga da shi .

Ya kamata kuma ya kula, ita ba watsatsiya bace da zai zo ya zauna kusan ƙugu da ƙugu da ita, har yana ɗaga mata waya yana fasawa, ita kam kallon farkoda tai masa ma ta liƙa masa taɓon tsumamme, mai baƙin hali. To yanzu kam ta ƙara da mugu ma.

Haka kawai ya fasa mata wayarta, kuma wai sai sannu! Kawai zai gaya mata, ga shi goshinta ji take yin sa gingirim haka da shi. Tabɗi! Hala ma yai mata ƙulu a goshi? Tsayawa ta yi a tsakiyar filin, ta fiddo madubinta daga jaka tana duba wurin.

Hular hijabin ta, ta ɗan jawo gaba, sannan ta ƙara duba madubin. Yana kallon abin da take yi, daga inda yake tsaye gaban kanta. Girgiza kansa ya yi haɗe da yin murmushi.

Abin da ya daskarar da shi kenan. Murmushi ya yi? Shi Masdook ya yi murmushi yau. Rabon shi da yin murmushi tun… Wani azaban raɗaɗi ne ya ji ya ziyarci zuciyarsa, wannan ya sa nan da nan ya kawar da tunanin daga zuciyarsa. Gyara zaman jakar komfutarsa ya yi a kafaɗarsa, sannan ya nufi ƙofar da ya ji an ambaci masu hawa jirginsu su ƙarasa.

*********

Tura jakarta ta yi wurin adana jakunku na, sannan ta miƙe bayanta a jikin kujerar, saboda ta gaji da zama, ga shi yanzu za su ɗauki kusan awa huɗu kafin su isa birnin Tel Aviv daga Frankfurt.

Duk ita ta janyowa kanta wannan damuwar. Su Faiz yanzu kam sun mance sun isa masauki ga ta ita har yanzu tana garari a ƙasashe. Ita ba ta san ma me ya kai ta amincewa da wannan aikin ba? Tunda ta karɓe shi, banda baɓar wuyar da take ci, babu komai a ciki.

Kasancewar Jirgin na Lufthansa mai tafiya Tel Aviv daga Abuja, ya sa dole suka biyo birnin na Frankfurt, inda za su shiga (Connecting Flight), jirgi mai kai su masaukinsu. Sannan ta rasa nata jirgin, saboda sakacinta, wannan ya janyo mata bin jirgin da aka jinkirta shi, saboda rashin kyawun yanayi, har ta kai ga kiran Abbunta don ya faɗa mata abin yi.

Ga shi yanzu wancan mugun mutumin ya fasa mata waya, ya kuma ce mata ‘Sannu’ tamkar daman ya saba fasawa mutane abubuwa, ya ce masu sannu, ya kuma share. To an ce masa ciwo take yi ne?

Sai a lokacin ta zabura, “Yau na shigesu, idan na isa, yaya za ayi na kirasu a waya kenan?” Tun farko ba ta san me ya kai ta tahowa ita kaɗai ba, ba ta taɓa jin tsoro ya shigeta ba a iya tafiye-tafiyen da take yi, to amma ba ta taɓa tafiya zuwa wata ƙasa ita kaɗai ba. Sai da su Abbu, ga shi yau garajenta ya kai ta. Kuma ba waya a hannunta.

Bata san lokacin da ta sa kuka ba, kuka abin ta take yi tsakani da Allah, ba abin da ya dameta. Duk da ba ihu take yi ba. Amma idan dai ka na kusa, za ka ji shessheƙar ta. “Wallahi komai ma ka ke gadara da shi, yau kam ka tare shi, ka samu. Haka kawai ka ɓatar da ni a ƙasar mutane. Yanzu yaya zan samu lambar su na kirasu?”

Tunani ɗaya ne ya faɗo mata ko ta sauka ta zauna a kasar Germany, kar ta yi aikin nata ko kuwa ta wuce Tel Aviv ta yi ta aikin zare idanu har ta ga wanda suka je karɓanta a filin jirgi.

Har ta tashi za ta fita ne, daga jirgin, sai kuma dabara ta faɗo mata, tunda ta san lambar Abbu da ka, sai ta kira shi. Ta faɗa masa abin da ake ciki, koda wayar kuɗi ce, idan ya so shi kuma ya kirasu, ya faɗa masu inda take.

Nan take ta shiga dariyar farin-ciki, ganin ta samo hanya ma fi sauƙi da za ta fita daga wannan matsalar. Duba gefenta ta yi, ta ga babu kowa, don haka take tunanin ko ba mai kujerar ne. A hankali barcin gajiya ya fara ɗaukarta. Ga zaman benci ga yunwa.

Ba a daɗe da fara tafiya ba, ta ji ana tambayarta me za a kawo mata?  Nan ta buƙaci shayi ko hanjinta za su ɗan warware, amma ba ta yi tsammanin za ta iya cin sauran abincin ba tuku na.

*********

Ɗan ƙararrawar da ke nuni da a ɗaura ɗammara, don shirin sauka ne ya hasko, wannan ya jawo hankalin Mihjana. Don haka ta buɗe idanu a hankali, ta yi yadda aka ce. Har yanzu ko ina ciwo yake mata a jikinta. Tunanin ta ɗaya, yanzu yaya za ta yi idan su Yinka ba su zo filin jirgin ba, kasancewar ta ce za tai masu waya idan sun taso?

Sai lokacin ta ga wautarta da tun a Birnin Frankfurt ba ta nemi wayar Abbu ba. Koda suka sauka, ana ta sauka zuciyarta kan abu guda take, don haka ta yi duk abinda ya dace ta yi, tunda jakarta babba na hannunsu Yinka, na hannunta kawai ta sauke, sannan ta nufi inda za ta samu waya haɗe da yin tambaya, saboda girman (Terminal 3) ɗin ga shi ya haɗu da ba ta taɓa zuwa ƙasar ba.

Abu ɗaya dai da ta sani, shi ne ba za ta taɓa barin wurin nan ba, sai a motar kamfani da filin jirgin suka yarda da su, don yanzu za a hallakata, musamman idan an lura da yadda take ɓari, don tsabar tsoro.

Wuraren cin abinci ta hango. Nan da nan ta ji cikinta ya yi ƙugi, amma ta fi buƙatar waya akan abinci a wannan lokacin. Cikin sauri ta isa wurin wayar.

Kamar ta yi fitsari da ta ji wayar tana ta ƙara, babu wanda ya ɗaga, yau ta shiga uku idan… ba ta ƙarasa tunaninta ba, ta ji muryar Abbu ya kwararo sallama. “Abbu ban san yadda zan yi ba, na shiga jirgin kamar yadda ka faɗa min, to amma Abbu tun a Germany wani mugu kawai ya je ya fasa min (Screen) ɗin wayata, yanzu ba na ganin komai ya yi baƙi, ba ni da lambar su kuma. Abbu ka na da lambar Mr Kamaal ai, kira ya ba ka lambar su, ka ce masu mun iso su zo su ɗauk…”

“Calm down! Mihjana. Ba abinda zai sameki kin ji? Kar ki firgita, yanzu ki na ina ne?”

“Ina ta wurin ƙofa ta biyu (2) ne.”

“To ki tsaya a nan, zan yi waya, sai su sameki ko? Sai ka ce ba ƙwararriyar ‘yar jaridata ba?”

Jin Abbu ya ba ta ƙwarin gwiwa, ya sa ta samu gefe guda wurin tarbar baƙin ta yi zamanta da jakarta tana jira. Can kuwa ɗaga kanta da za ta yi, sai ta hango shi cikin mutane, domin kuwa ya fita daban, daga tsawon sa da yanayin ginin jikinsa.

Duk da ya kusa sajewa da jajayen fatan, amma farin sa ya fi kama da na Larabawa, yanayin gyaran fuskarsa da kaurin jikinsa ne, ya sa ta yi saurin gano shi, domin kuwa  Mr. Abubakar ba irin mutanen da idan ka gansu karo na farko za ka mance su da wurin nan bane. Yana da dogon fuska da ya wadatu da cikakken gashin gira da kuma lallausar gashin da ya kwanta a gefe da gefen fuskar.

Yana da wasu idanu farare tar! Da sai an daɗe kan ka ga irin idanu masu haskensu, ga jajayen laɓɓansa da za ka yi tunanin anya yana magana da su kuwa? Domin tamkar na jarirai haka jansu yake. Hancinsa shi ya ba shi cikon kyawunsa, yadda yake da dogon karan hanci, wanda bai tafi sumul ba, irin dai na gogaggun mazan nan da suka cika da izza ne.

Baya ga cika, idon sa yana da wani abu a tattare da shi da bazata ce. Saboda ɗazu kam ta sha kallo, kafin ya gwara mata kai, ya kuma fasa mata wayarta, sai dai Allah ya yafe mata, take ta ce “A’u’zu billahi minasshaida nir rajim”. Da gudu-gudu sauri-sauri ta je ta same shi.

Ba ta taɓa farin-cikin ganin mutum ba a rayuwarta, kamar yadda ta yi a yanzu, don har ta fara tunanin ta zama nama a garin mutane. “Mr. Abubakar, tsaya tsaya. Ina ka ke tunanin za ka tafi ka bar ni?”

Juyowa ya yi yana dubanta haɗe da ɗan tsumewa kaɗan, cikin tattaro tunaninsa “Ka fasa min wayata, ka sa na rasa lambar masu zuwa su ɗaukeni, yanzu banda lambar su, sannan kuma ba su san ma jirginmu ya taso ba, sannan za ka gudu ka bar ni. Yau kam babu inda za ka tafi ka bar ni, na faɗa maka ƙafarka, ƙafata.”

Yau yana ganin ikon Allah. Shi tundaga Frankfurt, ya san ya gamu da gamonsa, ga shi har yanzu ba ta rabu da shi ba, don haka ya ƙare mata kallo, ka na ganinta, ka san a tsorace take.

“Ina kayanki?” Kawai abin da ya tambaye ta kenan.

“Me za ka yi da kayana?” Ta faɗa tana masa kallon rashin yarda.

“Za ki faɗa, ko kuwa kin fi son ki fara bara a Isreal? Idan dai ba so ki ke yi waɗancan yanzu su zo su yi awon gaba da ke ba, ki nuna min jakarki.” Harɗe hannu ta yi a ƙirji tana ta ɗagelgel tana leƙen ‘Yan-sandan da suke ta sintiri a filin jirgin ta saman kafadarsa, kuma da gani ba su da mutumci, za su iya kwasheta a kulleta a wani wuri a mance da ita, koda yake ai tana da shaidar aikinta a tare da ita, ba me mata komai.

“Ba ni da kaya.” Ta faɗa ƙasa-ƙasa.

Fuskarsa ya so ya yi abin da ya yi kama da murmushi, amma ko kaɗan ba za ta yi kuskuren kasafta hakan da murmushi ba, domin yadda ka san wani wanda aka kawo mai labarin mutuwa haka yake, sai dai wani abin mamaki, duk tsananin tsumewarsa, bai rage masa cika idonsa ba, ko kaɗan. Kamar ba zai yi magana ba, can kuma dai ya ce “To, biyoni.”

Bai jira ta ba, ya yi gaba abinsa, don haka ta fara gudu-gudu, don ta kamo shi, ganin baida da sassauci, maimakon ya rage tafiyarsa, tunda ya san ita ba ta da irin dogayen ƙafafunsa, amma ko a jikinsa, “To ai shi ma baida da kaya, banda jakar sa ɗaya ta rataye. Gwamma ni ma kayana na wurin Yinka” Ta faɗa a ranta, ganin shi singur da ta yi.

Suna zuwa, ta ga ya nemi Tasi ɗin kamfani. Ya juyo ya ce “Gabas ki ka yi ko yamma?”

Uhmm? Cikin zare idanu take kallon sa, don haka ya ɗan buɗe idanu cikin mamaki.  “Kar ki faɗa min ba ki san inda za ki je ba?”

Ka ji zai raina min wayo? Ɗauke kanta ta yi ta harɗe hannayenta a ƙirji Ta ce “To ko kai ka san gabas ne a ƙasar nan?”

Juya idanunsa ya yi cikin ƙosawa, ba abinda yake so irin ya rabu da ita, ya kama gabansa, don haka ya ce “Cikin Tel Aviv za ki shiga, ko Jerusalem ki ka yi?”

“Tel Aviv mana, ko kai ba jirgin can ka shigo ba?” Ta faɗa cikin ƙaguwa. Don haka gani ta yi ya buɗe ƙofa ya bar mata shi a buɗe, shi  kuma ya shiga gaba.

Ta soma tunanin anya kodai ta jira ne? To idan kuma Abbu bai samu su Yinka da wuri ba fa? Sai kuma ta ce “Duk dai muguntarka, ba za ka saida ni a ƙasar nan ba.” Har ta shiga motar, sai kuma ta canza shawara. “Ku maida ni, na tuna Abbu na ya ce zai turo a zo a ɗaukeni.”

“Shi ya sa na ga kin tsufa a masaukin ki. By the way, ina ne masaukin naki?”

Idanu ta zaro kafin cikin sauri ta tuno ta rubuta adireshin, gudun kar wanda yake wayar. Yinka ya ɓace masu.  Ga shi zai mata amfani, nan dai ta hau binciken Jakarta, can kuma ta fiddo ɗan ƙaramin kundin sirri ta miƙa masa. Da ta tuna da adireshin ma a rubuce da kai tsaye ta wuce masaukinta, ba ta tsaya nema masa ba.

Sai da ta miƙa, sannan ta ce “Farkon kawai za ka kalla, kar ka buɗe min littafina.”

Girgiza kai ya yi, ya miƙo mata ba tare da ya ce komai ba, ganin ta tsaya kallon sa, ba ta da niyyar motsawa,  ya ce “Buɗe da kanki.”

Da sauri ta wafce ta buɗe, ta miɗa masa. Da ya gama dubawa ne, ta ga ya yi magana da direban. Sannan suka ci-gaba da tafiya. Saman kansa take hangowa ta saman kujerar, da kuma kafaɗun sa. Ko me ya zo yi, oho? Ita dai damuwarta, ta samu ta ga ‘yan-uwanta su Yinka.

Kamar daga sama ta ji ya ce mata “Me ki ke yi a ƙasar nan ke kaɗai?”

“Aiki na zo yi, kuma ba ni kaɗai bane, saboda haka idan ma sayar da ni za ka yi, to akwai waɗanda za su zo suna nemana, asirinka zai tonu.” Murmushi ya yi, yanzu kam sosai, har haƙoransa suka bayyana. A ransa ya ce “Ai ko ke ta sayarwan ce, ba me sayenki.”

Tana ganinta a masauki, bayan kusan tafiyar minti talatin da suka yi, ta sauke ajiyar zuciya, har ma ta ji kamar ta yi ihun daɗi. Tana sauka daga motar, ta juyo ta ce masa “Na gode, Allah ya biyaka, duk da dai kai ka janyo min.” Ba ta jira me zai ce ba, ta zari ‘yar jakarta ta yi cikin Otel ɗin.

Ya rantse da Allah bai taɓa ganin mutum irin yarinyar nan ba. Ba ta da damuwa sam a rayuwa, ya ga alama, kuma daga gani ta saba samun abin da take so. Amma nan take ya ji ya tsaya, ya ga ta samu abokan tafiyarta ko kuwa?

Koda yake menene ruwansa da ita? Don haka ya juyo ya faɗawa direban adireshin na sa masaukin, inda ya yi masauki a Otel din Sheraton.

Yana isa ɗaki ruwa ya sakarwa kansa, ya nemi abinci, sannan ya shiga aiki, yana gama abin da yake yi. Ya ce “Saura kawai ki zauna cikin yanki mai sabis kin gama min komai!”

*************

TEL AVIV, ISRAEL.

25 YULI 2010 — 2:08 AM

Tun haɗuwarta da jama’arta, bayan sun tafi filin jirgi, sun yi ta yawon nemanta ba su sameta ba suka dawo, nan suka zo suka tarar da ita a zauren karɓan baƙi tana ta narkan barci, “Tunda Ummi ta haifeni, ban taɓa wahalalliyar tafiya irin ta yau ba.” Abin da ta faɗawa Yinka kawai kenan. Sannan ta miƙe ta bi bayansu, inda aka nuna mata ɗakinta, ba wani babban ɗaki bane.

Otel ne mai lambar yabo uku, ba laifi yana cikin gari, sannan kusa yake da kasuwar raƙuma, da abubuwan tarihi na ƙasar wanda musabbabin abin da ya kawo su kenan, wannan ya sa suka kama masauki ta wannan yankin garin, da kuma tattalin aljihun kamfani. Kowannensu da ɗakinsa.

Banɗaki ta wuce da sauri ta rage mararta, sannan ta sakewa jikinta ruwan zafi ta gasu sosai, kafin ta ɗauro alwala ta fara biyan sallolinta.

Koda ta idar, ashe ko motsawa ba ta sake yi a wurin ba, nan barci ya yi awon gaba da ita, sai yanzu ta farka, a sanadiyyar wata tsuwwa da take ta ji tana fita, ta rasa daga ina. Ta gama sauraron ko ina a ɗakin, amma ba ta ji daga ina ƙarar ke fitowa ba.

Can kuma ta sake jin wata daban, sai lokacin ta fahimci ko na menene wannan, wayarta ce take ƙoƙarin mutuwa, nan ta ƙara jin haushi.  To ai daman da ke da babu duk ɗaya, gwamma ki mutu na san cewa caji ne ya ƙare.

Koda ta farka ma dai, ta gaji da yawa, da har take ganin tauna abinci ma zai ba ta wahala, don haka ta koma saman gado ta ci-gaba da lafiyayyen barcinta, ko Abbu ma ba ta kira ba, sai da safe kawai.

*********

SHERATON HOTEL 2:35 AM

Ya kamata yanzu hutawa zai yi, kafin zuwa safiya ya wuce wurin taron, amma ya kasa hakuri. Nan da nan ya koma ya buɗe shafin da yake aiki a kai ɗazu, sai da ya ci ƙarfin abin da yake gudanarwa, sannan ya rufe na’urar.

Wayarsa ya janyo zai yi waya, sai ya tuna baida da lambar a wannan wayar da ke hannunsa, haka kawai sai wannan yarinyar ta faɗo masa a rai. Girgiza kai ya yi kawai, har yanzu bai san sunanta ba, bai san daga inda take ba, da kuma irin aikin da ya kawota. Ba abinda ya sani game da ita, baya ga cewar ita karan kanta damuwa ce ko yace babbar matsala.

Wannan ya sa ya ajiye a ƙwaƙwalwarsa cewa daga ya fito daga taro, zai sameta a inda take. Kunna ƙira’a ya yi a wayar tasa, ya kwanta cikin shirin barci, ba tare da ya kashe ba.

*************

“Yinka kin faye nuƙu-nuƙu!” Mihjana ta faɗa cikin ƙosawa da abokiyar aikinta da ta gaza gama shiryawa su tafi yin abin da ya kawo su.

“Dole ki ce haka, na ga dai ba ni bace na rasa jirgi na.”

Juya idanu ta yi ta ce. “To kuma sai aka ce ki yi ta tuna min, duk sanda ki ka ga dama ko? Me ya shafe ni, kin san Faiz sarai ko minti biyar muka ƙara ba mu sauka ba, tafiya zai yi ya bar mu.” Ta faɗa tana cusa bironta cikin aljihun jakarta, haɗe da littafi ɗan madaidaici.

Kayan ɗaukar hoto da sauran na’urar da duk za su buƙata suna wurin Faiz da Williams (Guide) ɗinsu, mai nuna masu gari. Don haka ba ta jira Yinka ta saka makeken sarƙar duwatsun da take kokuwa da shi ba, ta yi gaba tana faɗin “Wai duk haka ku ke ne Yarabawa da ɗaukar kwalliya kamar wani hidimar biki za ki je?”

Yinka ba ta ce komai ba, ta san halin Mihjana sarai da tsokana da kuma zolaya, wannan ya sa ta shiga ran kowa a ofis ɗinsu inda suke aiki, da tashar nan fitacciya (Exclusive Life). Duk da dai da farko sai kun yi faɗa, daga baya za ka zo ka fahimci cewa haka Mihjana take, kuma nan da nan za ka so ta.

Kyakkyawar Bafullatana ce, mai siririn mulmulallen jiki da ƙaramin fuska, ba ta vda girman kai, ko jiji da kai, don ita idan ka ce Mihjana ta yi digiri na ɗaya da na biyu, sannan ta yi shekaru biyu tana aiki, ba za ta yarda ba, idan an bar ta, bai wuce ka ji tace tana aji ɗaya a jami’a ba.

A shekarunta ashirin da shida a duniya, ta kan shammaci mutane da dama wanda suke ba ta shekaru sha takwas. Fara ce ‘yar luwai-luwai da ita, ba za ka ga wani kyawunta ba, wanda zai sa nan da nan ka so ta.

Baya ga farin fatarta, tana da idanuwa masu kyau da ɗaukar hankali, hancinta bai faye tsawo ba, sai dai ba laifi akwai kara. Idan ta yi murmushi, to tabbas za ta sace zuciyar mutum da kyawawan jerarrun haƙoranta farare tas sirara.

Kullum yanayin shigarta kuwa, daga hijabs sai jilbaabs da dogayen riguna. Yinka ba ta taɓa ganinta da wata banzar shiga ba, wannan ya sa ta taɓa tambayarta ko ita matar aure ce?

Mihjana murmushi kawai ta mata, ta canza salon hirar ta su da cewa, haka ake sa kaya a addininta. Yinka daga nan ta ji Mihjaana ta burge ta, domin kai tsaye take komai tsakani da Allah, babu zancen ɓoye-ɓoye.

Gata da ƙwazo kan aikinta, domin ko batun tafiyar nan, sai da ta sha wuya sannan aka bar ta ta taho, amma ba ta karaya ba, saboda aikinta na gaba mata da komai. Idan tana turanci kuwa, ba mai cewa a Najeriya ta yi karatu, ta iya Faransanci, ranar kuma ta ji ta tana larabci da wata ‘yar rahoto Basuda niya.

Wannan ya sa ta mamakin wai menene abin da yake sa Mihjana Suraj Suyudi take isa inda ta kai a rayuwa, ba tare da ta bari wuyan ya nuna a tare da ita ba? “What makes her tick?” Kallonta ta yi a yayin da ta matsa gefen Williams tana gaishe  shi daga nesa.

Ta taba tambayarta, me ya sa ba su gaisawa hannu da hannu da maza, ita kuwa ta ce mata “Me ya sa ki ke gaisawa ke?” Shiru ne amsar, wannan ya sa take mata ganin GIRMA! Duk da kuwa ta fi ta a shekaru.

“Oh, Fa’iz yanzu ba za mu karya ba, za mu wuce?”

“Kin duba agogonki kuwa?”

“Na sani, mun yi latti, amma fa jiya ba ka san wani irin wahalallen barcin da na yi ba.”

Gintse dariyarsa ya yi, bai dai son ta gane abin ya ba shi dariya ne, amma ya so ya ganta a filin jirgi da suka tafi suka bar ta a Frankfurt. Kawai daga an jinkirta tashin jirginsu suka bazama yawo a filin jirgin, suka yi ciye-ciye, Mihjana ta shiga banɗaki sai ta kulle ta ciki, su kuma sun yi gaba, a tunaninsu ta shiga layi. Sai da suka yi (Boarding) suka kula ba ta ciki.

Nan ne suka kiɗime, Yinka na duba wayarta ta samu (Missed calls) kusan goma sha uku, ashe wayar tana (Silent) ne. Dole ta bari sai sun sauka, don ba damar su yi waya, sun riga sun tashi.

“To na ji za mu tsaya cin abinci, amma ba latti yau za mu fara zuwa Bauhaus Tour da Independence hall, kafin nan idan da sauran lokaci mu je tsohon Jaffa kamar yadda Williams ya faɗa.” Yai masu bayani cikin turanci.

Wannan ya sa Mihjana ta maida hankalinta ga tagar motar inda suke wuce gine-gine masu ban sha’awa, kafin su tsaya dai-dai wani madaidaicin gidan cin abinci, yanzu ne ta ji ba ta ji haushin Faiz ba, da ya hanasu cin abinci daga masauki, saboda kallo ɗaya ta yi wa wannan wurin, ta ji ya burgeta.

Kusan awansu biyar suna yawo. Williams yana masu bayani a duk inda suka tsaya. Yayin da Yinka take naɗan duk abinda yake faɗi. Fa’iz yana ɗaukar hirar Mihjana da Williams inda take masa tambayoyi, game da al’adu da sana’o’in garin dama mutanen garin baki ɗaya.

Zuwansu Bauhaus Center, ƙwarai ya ƙayatar duk da turancin mata mai maganar baya fita sosai, amma sun ga abubuwa masu ban sha’awa da kuma matuƙar muhimmanci a wannan shiri da tasharsu take shiryawa game da bambancin al’adu na ƙasa daban-daban a faɗin duniya.

Kafin ƙarfe huɗu sun zaga muhimman wuraren da ya dace a cikin shirin na su, sun kuma ƙaru cikin ilimi da wayewa, kan rayuwar jama’ar garin.

Ƙwarai Mihjana ta gaji likis! Ga gajiyarta ta jiya, don haka ba abinda take muradi irin ta samu ruwan zafi, ta gasa jikinta ta miƙe.

Sun gama cin abinci a wani buɗaɗɗen gidan cin abincin da aka jera kujeru a waje, yayin da wasu masu nishaɗantarwa suke ta faman aikinsu na busa algaita irin dai na al’adar mutanensu. Mihjana tana son su koma masauki, yayin da Yinka kuwa ba ta ƙi su kwana  a wurin ba, ta yi ta yi kallo.

Kamar da wasa, ta sake jin wannan ƙarar da ta ji tun jiya da dare. Ta shiga waige-waige. Can ta ce “Wayar waye a cikinku take ƙara?”

Dukkansu kowa ya dubi tasa wayar amma babu mai ita. Don haka ta cire abin a ranta. Sun miƙe da shirin tafiya ne kawai, ta tsaya cik! Fa’iz ƙwarai ya tsorata, ganin yadda fuskarta ya nuna alamu na tsantsar razana.

Kafin lokaci guda, ya ga ta rikiɗe ta koma fuskar faɗa, bai samu damar tambayarta abin da ke damunta ba, ya ga ta fita daga cikin kujerar ta isa wurin wani mutum.

“Yau na ga ikon Allah, bi na ka ke yi ko menene? Don kawai na roƙeka ka taimakeni, shi ne za ka yi ta bina duk inda na je a gari?” Zai yi magana ne, ta sake katse shi.  “Ko kuwa ka na so ka ce kai ma abin da ya kawo mu ƙasar nan, shi ne ya kawo ka, idan ba haka ba, yaya za mu haɗu a filin jirgi, mu shiga jirgi ɗaya mu sauka gari ɗaya, sannan na fita yawo duk girman garin nan, na sake haɗuwa da kai?”

Su Yinka dai mamaki ya hana kowannen su motsi. Shi wanda ake ta bidirin dominsa kuwa, bai ce mata komai ba tukun, sai da ya yi taku biyu zuwa gareta, da sauri ta ja da baya. “Lafiya?”

I believe you have something of mine. (Ina da tabbacin akwai abi na da yake wurinki).” Mihjaana kam juya idanu ta yi, don ta san halin irin mutanen nan sarai, suna haɗuwa da mutum, to zancen ɗaya ne, ko a nemi lambar wayarki ko kuwa kawai ki ga ana ta turo miki saƙwanni ta ko wane kafofin sadarwa.

Don haka ta ce. “Idan ma tunaninka shi ne ka cutar da ni ko ka yaudareni, na faɗa maka tun jiya ba ni kaɗai na zo garin nan ba, don haka kar ka ji da wai. Na san me yake ranka sarai. Kuma ba za ka samu ba, duk maza daman tunaninku ɗaya ne, bai wuci ka ce kai ba haka ka ke nufi ba ko? To bari ma ka ji ni matar aure ce.” Ta faɗa cikin jaddada masa maganarta haɗe da ɗaure fuska tamau! Ta kwaikwayi tsayuwarsa haɗe da ɗaga haɓar ta sama cikin ɗagawa.

Shi kam gyara tsayuwarsa ya yi, hannayensa bisa ƙirji ya gama jin ɓaɓatunta. Faiz kuwa har da naɗe hannun riga ya yiwo gaba zai ji dalili, tunda dai sun gan shi fari tas! Ga shi turanci ya yi, ba su ma zaci ɗan Najeriya bane.

Da sauri Mihjana ta hana shi, ta hanyar ɗaga mai hannu ta dakatar da shi “Kar ka damu na san maganinsa, ina jinka ka faɗa min me ye ka ke nema da ni, da ya sa ko ina na je ka ke biye da ni. Na gode da taimakon ka na jiya, amma don Allah na gaji da ganin fuskarka haka nan.”

Yanzu kam kallon kura yake mata, don ba ƙaramin haushinta yake ji ba, za ta tara masa jama’a, duk matsayinsa, koda yake ba kowa bane ya san ko shi waye, amma mutumcinsa ba abin zubarwa bane, koda daga bakin kyakkyawar ‘yar mitsilar bafullatanar  ce,  ko matar da take yawon ƙasashe tana yin koma menene, oho? Wanda mijinta baida da kishin kai, balle kishin iyalinsa, ya bari matarsa tana yawo a filayen jirage, tana ɓata ba tare da muharraminta ba, tana sa’insa da Ajnabi ɗinta.

A take ya ji ya tsani mijin, tun kan ya gan shi da ita kanta ‘yar mitsilar, haushi take ba shi. Wayarsa ya ɗaga ya daddanna wasu lambobi. Nan take kuwa ta ji wancar ƙarar tana yi, koda ta saurara, sai ta ji daga jakarta ƙarar ke fitowa. Wani sauti kamar ana sheƙa ruwa.

Ɗaga mata gira ɗaya ya yi cikin alamar tuhuma “Ki amsa mana ko ba wayarki bace take ƙara?”

“Wayata?”

Nan da nan ta sa hannu ta ciro wayar daga jakarta, sai kuwa ta tsorata, yaya aka yi wannan wayar ta shiga jakarta?

“Na yi zaton jiya za ki buƙaci magana da wasu na ki, shi ya sa…” Sai lokacin ta yi shiru cikin tunani, wato lokacin da ta ji kamar an taɓata, jakarta aka buɗe kenan.

“Kai ka buɗe min jaka, wato irin ku ne masu Smuggling abu a cikin jakunku nan jama’a ba tare da saninsu ba!” Ta faɗa cikin masifa. Girgiza kai ya yi, wannan yarinyar… au mata ce ashe, anyi mahaukaciya koman ta faɗa da masifa da surutu. Yana tausayawa koma wanene mai ita.

“Phone…” Ya faɗa yana nuna mata wayarsa. Nan da nan ta miƙa masa tana goge hannunta a gefen kayanta, wanda ya jiƙe da zufa, saboda wata irin kunya ce ta rufe ta. Amma ba za ta taɓa bari ya gane ba.

Shi kuwa ya sa hannu ya buɗe zip ɗin jakar hannunta ya saka mata sabuwar kwalin waya a ledarta ma take, ya zuge mata zip ɗin. Mamakin ƙarfin halinsa ya hana ta magana a karo na farko. “Yaya za ka buɗe min jaka, bayan gani a tsaye a gabanka?”

“Ban san koma waye ya koya miki yin godiya ba, amma koma waye ne, na tausaya masa, domin har yau kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, (He sucks!).”

Yana faɗa mata haka, ya juya, kamar kiftawar ido, ta neme shi ta rasa cikin hayaniyar filin kasuwar.

Juyowa ta yi tana duban Yinka “Kar ki faɗa min abin da ya faru yanzu da gaske ya faru? Ba mafarki na ke yi ba!”

Yinka tana dubanta da sakakken baki da buɗaɗɗen hanci da idanu ta ce “Arh… idan ki ka yi la’akari da yanzun nan aka ba ki kyautar wayar Naira dubu ɗari uku, zan iya cewa, idanunki a buɗe suke tangararan! Kar ki damu, haka na faruwa idan ka samu irin kyautar musamman daga mutumin da ba ka sani ba.”

Sam hankalin Mihjana ba a kan Yinka yake ba, balle ta fahimci me ma take faɗa. “Yaya za ayi ya ce min ban iya godiya ba? Yaya za ayi ya taɓa min jakata? Wai ma yaya aka yi ya san inda muke? Anya ba Aljani bane kuwa mutumin nan?”

Yinka ba ta saurarenta, domin a daidai wannan lokacin jakar Mihjaana take buɗewa ta fiddo kwalin wayar da aka sawa ƙawarta a jaka tana shafawa “OMG! Porsche, kyautar Porsche yai miki yanzun nan!” Ba ta kula Yinka ba, hankalinta ya gama tashi. Da fushi da wannan Mr. Abubakar ɗin nan, idan ma yana da suna ma kenan.

Abin da ta sani kawai, tun jiya ya damu rayuwarta.

Muryar Fa’iz ta ji a daf da kunnenta yana cewa “Akwai abin da ake cewa ‘Tracker’ ko kin san da shi? Maɓalli na samo wayar da ta ɓace. Saboda haka samo ta ki, ba wata gagarumar matsala bace a gare shi, musamman idan ki ka yi la’akari da mutumin ya san me yake yi.

Saboda yana da hanyar samo wayarsa, a duk inda take, muddin akwai (Network) a wurin, kuma ta hakan ya sameki. saboda haka ki kwantar da hankalinki. Ki more sabuwar wayarki. Gobe sabuwar rana ce, kuma muna da aikin yi.”

“Porsche ya ba ki! Ko hala ma yana da guda nawa, sai Allah, ko ma ya mallaki irin motocin, wa ya sani. Ke kin san waye ma ki ka haɗu da shi kuwa? Ko kyafta idanu bai yi ba ya baki kyautarta. Don Allah duba ko ya sa miki lambarsa a cikin wayar.” Duk da turanci Yinka ke ta wannan ɓaɓatu da zuban kamar ruwan sama.

“Ki riƙe wayar na ba ki.”

Nan suka wuce suka bar Yinka rungume da kwalin waya a ƙirji, da sakakken baki.

Rai a bace ya bar tsohon Jaffa, tun safe yake bin motsinta, duk da ya san ya bar ta jiya lafiya, amma yana ta tunanin kar ba ta samu abokan tafiyarta ba, ko kuwa ta sake ɓata, me ya sa bai tsaya ya ga ta shiga hannun da ya dace ba? Da wani abu ya sameta fa? Nan take ya ji ya kareta, tamkar yadda babban yaya zai kare ƙannensa.

Saboda bai yi tsammanin zai iya jure wani ya sake shiga ha’ula’i a dalilin rashin kulawarsa ba, wannan ne tunani na farkoda ya shige shi, ko jiya a filin jirgin, hakan ya sa  ya saka mata wayarsa a jaka, don ya san idan ya ba ta, ba za ta karɓa ba, shi kuma ya san a wannan yanayin, waya ce kawai abin da za ta bawa mutum natsuwa, idan ya samu magana da wanda ya yarda da su.

Sun kammala taronsu da wuri, amma akwai wasu abubuwa da ya dace ya kammala, a matse ƙwarai yake da samun wasu lambobin, hakan ya sa ya yi tunanin zuwa masaukinta na jiya, wato (Galilio Hotel), sai dai ta ce aiki suka zo yi, idan suka yi saɓani fa? Ba ɓata lokaci, ya kunna Tracker ɗin wayar tasa da ya jona da komfutarsa.

Ya sha wahala kan ya riske su, saboda yawon da suke yi a gari. Bai tabbatar da aikin suke yi ba, sai da ya gan su da idanunsa. Yarinyar akwai bakin tsiya, ko yau ko gobe zai so ya yi maganinta.

Amma a halin yanzu yana da matsalolin da suka fita girma. Kamar samun kwangilar da yake nema tare da kamfanin jiragen! Duk da ya taho domin halartar taron   shekara-shekara da aka shirya na cikon shekaru hamsin a Israel (50th Annual Conference). Akan kimiyyar sararin jiragen sama (Aerospace), wanda za ayi na kwanaki biyu a Tel Aviv da birnin Haifa.

Musabbabin zuwansa, domin ya damƙi wannan kwangilar ne wa kamfaninsu wanda yana ɗaya daga cikInshahararru a duniya baki ɗaya, a matsayinsa na fitaccen Injiniyan kwangila kan harkar ƙere-ƙere da kula da harkokin jiragen sama (Project Engineer, Aeronautics) wanda yake aiki da kamfanin (Air Bus and Air Bus groups).

Don haka nan Masdook ya goge tunanin ‘yar mitsilar bafullatana mai masifa daga ƙwaƙwalwarsa.

Lambar Adir ya danna, kusan ƙara uku ya yi, sannan aka ɗauki wayar a ɗaya ɓangaren.

*********

ABUJA, NAJERIYA

02 AUGUSTA 2010 —7:45 AM

Tundawowarsu take ramakon barci, don yau kam ko aikin ma ta haƙura ba ta fita ba, shigowar Yasmeen ne ya sa ta motsa, “Don Allah kashe wutar nan ko zan runtsa.”

“Yaya Mihjanaa, Ummi wai barcin haka ya isa, ki sauko Abbu na nemanki.”

“Urgh! Yanzu barcina ya ƙare kenan? Ina son na yi barci.” Ta faɗa cikin turɓuna fuska.

“Ki je ki ji menene ne, to sai ki dawo mana.” Cikin fushi-fushi shagwaɓa-shagwaɓa ta fita daga bargon, ta ɗaure gashinta da ya wargaje da Ribbon, sannan ta ɗaura zani saman kayan barcinta, ta nemi hijabi ta ɓurma, duk da ta san Abbu ya tsani su kai ƙarfe taran safe suna kwance, ta sani ba zai mata faɗa ba, tunda ya san jiya suka dawo a gajiye.

Sallama ta yi ta shiga falon, nan ta same su, saman teburin cin abinci, ita ma kujera ɗaya ta ja ta zauna. Sannan ta shiga gaishesu. Abbu ya bi ta da idanu ya ce “Yaya na ga haka, ba ki shirya ba?”

“Abbu haƙarƙari na da kwankosona ne suke min wani wahalallen ciwo, shi ya sa nace ko yau ɗin zan huta ne, sai gobe na yi (Reporting)?” Ta faɗa cikin karkace wuya don a ƙyaleta.

“Mihjana, ba na son wasa da lamarin aiki, a ƙa’idance yaushe ya kamata ki koma aiki?”

Lissafi ta yi cikin nazari, ta ga ko yau kwanan wata menene? Don ita kam duk ta birkice lissafin ya kwaɓe mata. Zaro idanu ta yi ta ce “Abbu mugaye ne mutanen nan, yau fa suke so na koma. Abbu Wallahi ban da lafiya.”

Dariya duk suka yi, saboda kaf gidan kowa ya san irin rakin Mihjana, shigowar Hajiya ne ya sa ta ɗan shiga taitayinta. “Ke tashi ki je ki shirya, kin cikawa mutane kunne da surutu.”

“Allah, Hajiya ko na je ofis ɗin barci zan masu, don haka gwamma ku bar ni kan katifar ma zan fi saurin warwarewa da wuri, musamman idan kin dafa min wannan farfesun na ki na Talo-Talo.” Ta faɗa haɗe da saƙale hannayenta a wuyan Hajiyar ta baya, tana neman yin lilo.

Ummi ce ta maƙe mata bayanta ta ce “Ka ji tsabaragen rashin kunya, Hajiyar sa’ar ki ce, sauka ki ba mu wuri da Allah.“ Ita kam ta gode Allah da ya bata iyaye masu matuƙar ƙaunarta da kuma ji da ita.

Hajiya da Ummi ko ba wanda zai gansu ya ce ma kishiyoyi ne, duk da kuwa yadda auren Ummi da Abbun ya kasance, amma Hajiya ta riƙeta hannu bibbiyu, suna zaune lafiya ta danne zafin kishinta, ta rungumi ƙaddara, sai ta samu sauƙin zama, hakan kuwa ya ƙara mata kima a idanun Abbu, don haka dukkan lamuran Hajiya baya taɓa ɗaukansu da wasa.

“To ‘Yan mata na idan kun gama daka ta ‘yar taku za ku kula da ni, wata ta yi Serving ɗina ko kuwa yau na fice da yunwa?”

“Distinguished, ai ba za a yi haka ba. Me ya yi zafi?” Hajiya kam kujera ta ja ta shiga tsiyaya masa ruwan zafi za ta haɗa mai ganyen shayin da ya fi so, yayin da Ummi ta shiga zuba abincin cikin faranti mai ɗan faɗi.

Kallonsu yake yi, kowacce ta sha wankanta gwanInsha’awa, ga ƙunshi nan a hannayensu ya yi baƙi wuluƙ. Hajiya dai kanta a rufe yake ruf, da ɗan-kwalin atamfarta ta kashe ɗauri, ba za ka ce shekaru talatin da biyar da suka wuce bane aka kawo masa ita a matsayin amaryarsa.

Yayin da Ummi kam ta zizaro kitson gaban nan ya kwanto ta gefen fuskarta, har yana taɓo ƙashin wuyanta, ita ma dai ɗaurin ta yi, duk da dai ita ba atamfa bace a jikin nata, wani rantsattsen leshi ne.

Shi kam lamarin gidansa, ba abinda ya kai shi daɗi a gunsa, domin duk inda ya je a duniya Allah-Allah yake yi ya dawo wurin ‘Yan matansa, kamar yadda yake faɗa masu.

Senata Faruk Ingawa kam, zai iya cewa ya samu abin da yake nema a rayuwa, muƙamai dai na girma ya tattaka su daki-daki har ya kai zuwa yanzu a Najeriya matsayinsa na ɗan majalisar dattijai.

Ga kyawawan matansa, ga yaransa. Maasha-Allah! Sai dai duk waɗannan abubuwa da ya tara, sun gaza gushe masa baƙin-ciki ɗaya na rayuwarsa, wanda ya yi masa dirar mikiya shekaru huɗu da suka shige.

Ko yanzu da abin ya zo masa ransa, nan take ya ji hannunsa ya fara kakkarwa, zufa ta fara tsattsafo masa. Ummi ce ta kula da yanayin da Mai-gidan nasu ya shiga, ta ce “Distinguished, lafiya kuwa, me yake faruwa?”

Da sauri ta zuba ruwa a tambulan, ta miƙa masa, ya samu ya kurɓi kaɗan. Hajiya koda sauri ta miƙe ta ɗauko maganinsa ta ɓalla ta ba shi.

Murmushi ya yi na ƙarfin hali ya ce. “Muddin ina tare da ku duka, ba abinda zai same ni, Insha-Allahu. Na gode. Allah ya bar min ku, ya ƙara haɗa kanku, ku ci-gaba da nuna min kulawa ta musamman.”

Ummi kam kunya ce ta hanata amsawa, ta yi shigewarta ciki, nan ta bar su da Hajiyar ko ba komai, ta san Hajiyar za ta fi rarrashinsa, kuma abin da yake damunsa, ya dameta amma ta san Hajiya za ta fi fahimtar ciwon sa fiye da ita.  Ƙwalla tashare ta wuce ɗakinta.

Mihjana tunda ta koma ɗaki barcinta ta koma, cikin barci take jin wayarta na ƙugi, cikin yanayin barcin har yanzu, ta ɗaga za ta danna ta a (Silent), amma sunan da ta gani ne, ya sa ba shiri, ta miƙe ta zauna dabas! Akan gadon.

“Hello, Sir.”

“Hello, Mihjanaa meet me in the office now! (Ki sameni a ofis yanzu nan).”

Ai kafin ya ƙarasa magana, ta buga tsalle, ta faɗa banɗaki da gudu, a cikin kayan wanki ta wurga wayarta, ta shiga cire kaya tana tara ruwa, tana (Brush) a tare, yau ta shiga magana. Nan take ta shiga lissafi minti nawa zai kai ta wurin aikinta da ke (Wuse Zone 5)? Maganinta kenan, tun ɗazu ake ta ce mata ta tafi wurin aiki, tana aikInshagwaɓa, sai yanzu ta kula kwankwason nata ma ya sake ya bar ciwo. “Ɗan kwasti, wato dama bai ga haza bane.” Ta faɗa a ranta.

Cikin minti uku ta gama wanka, ta fito, daga tsaye ta yi shafa ta ɓurma kayanta, Powder kam da man baki da wayarta, duk cikin jakarta ta ɗura, ta sauka a guje kamar an korota, bin ta kawai suka yi da kallo.

“Na tafi, Mr. Kamaal ya kirani.”

Ayaba kawai ta ɗauka kan teburin ta fice, ba ta ma ji me suke faɗa ba, to amma me zai sa Mr. kamaal ya kirata yau cikin gaggawa, bayan ya san jiya suka dawo? Kodai har Fa’iz ya kawo rahoton tafiyar da suka yi ne? Aikin ta ne ba shakka bai masa yadda yake so ba ɗila, dama kowa ya san Mr. Kamaal, komai zai yi, ko za ayi masa ya fi son ya gan shi cikakke.

Addu’a ɗaya take ta yi Allah ya sa ba kwafsi ta yi ba, adana motarta ta yi, sannan ta gyara fuskarta ta kimtsu. A tsanake ta fito ta shiga cikin ginin. Kai tsaye ofishin mataimakin Daraktan tashar ta nufa.

Kansa na duƙe kan wani aiki ta same shi, ɗakin ya gauraye da sanyi mai ratsa jiki, har yanzu tana tunanin yadda mutum zai iya jure irin wannan sanyin a cikin ƙashinsa. Wani Ƙato ne a tsaye kuma kakkaura mai duhun idanu, kansa a suɗe tal! Ga wani saiko a kansa, fuska raɗa-raɗa a shimfiɗe a fuskarsa, irin mutumin da ba za ka so ka na farkawa a barci ka yi arba da shi ba, don sai ka zaci masu garkuwa da mutane ne (Kidnappers) ne suka yiwo maka asubanci. Wa ya ga Basamude!

A karo na farko ba za ka taɓa cewa yana da wani matsayi ba, balle ka ce ma mahaifinsa ke da wannan shahararren tashar talabijin ɗin. Wannan ya ƙara sa Mihjanaa mamakin kiran da ya yi mata.

“Ina kwana.” Ta faɗa ta hanyar gaisuwa, tana daga tsaye a gefe.

“Samu wuri ki zauna.” Bai jira komai ba, ya ce “Yaya hanya? Yau zan karɓi rahotonku na duba shi da kyau, da daukar hoton, duk da dai ba na shayin samun aiki mai kyau daga tawagarku. Da fatan kun warware gajiya?”

Ita dai iya saninta, ba ta taɓa haɗuwa ita da Mr. Kamaal don su tattauna wani abin ba, komai ta hannun furodusan shirinsu yake zuwa wurinta, don haka ƙwaƙwalwarta ta fi matsa mata da tambayar ko me take yi a zaune a nan?

Ai kuwa Mr. Kamaal bai ɓata wani lokaci ba, ya ce “Muna da (Exclusive Interview), hira ta musamman ne da babban baƙonmu ranar Asabar mai zuwa, ban san ko za ki iya ba? Idan ba ki gaji ba kenan.”

Bakinta ne ta buɗe cikin tsantsar mamaki, yau ita ake bawa wannan fage na musamman ɗin, domin ta gudanar? Ai wannan ba ƙaramin ci-gaba bane a ɓangaren aikinta. Wannan yana nufin an yi mata ƙarin girma kenan. Duk da mafarkinta kenan, sai take tunanin yaya za ayi ta ma fara yin hirar?

“Amma, Mr. Kamaal sau ɗaya na taɓa…”

“Na yarda da ke, na san za ki iya, na ga ayyukanki. Zan dai ba ki wasu tambayoyi ki je ki duba, sannan ki ɗan yi bincike kan wallafe-wallafen da aka taɓa fitar da su da baƙinmu a ciki, ina ga zuwa yanzu dai abin da za ki buƙata kenan, ki samu furodusan shirin ku ƙara tattaunawa.”

Mihjana kam baki ya ki rufuwa, sai yaƙe shi take yi kamar gonar auduga. Godiya take ta zubawa, nan ta karɓi babban fayil ɗin hannunsa da ya miƙa mata. Akan ta je ta yi nazarinsu, saura ƙiris! Ta fice a guje, don murna. Ina ruwan garaje ga dami. Yace a sa miya.

Ofis ta wuce, kamar ko ta san za ta tarar da Yinka, don ita kam ba ta sanya, can ta fesa mata labarin abin da yake faruwa.  Ai Yinka kam tsallen ta daka hannunta riƙe da na Mihjaana, sai da aka juyo ana kallonsu ne, ya sa suka rage sauti, suka shiga dariya ƙasa-ƙasa.

“Mihjana, kin san abin da hakan yake nufi kuwa?”

“Ƙwarai kuwa, bari ki ga yanzu na kira Abbuna na faɗa masa abin da ake ciki, na san ba wanda zai kai shi farin-ciki.”

“Amma daga wane ɓangare ne mutumin da za ayi hirar da shi yake?” Yinka ta tambaya cikin son jin ƙarin bayani, domin kowa ya san wannan fagen ne yake gabatar da manyan mutanen Najeriya da suka yi fice a sashe-sashe na ci-gaban rayuwa, kama daga fannin nishaɗantarwa, siyasa, kimiyya da kuma al’adu da rubutun adabi.

“Ina ga dai Mr. Kamaal ya ce min INJINIYA MASDOOK ABUBAKAR ne, ni dai ban san shi ba. Ko ta yaya, ya ba ni fayil zan je na yi bincike zuwa ranar Asabar.” Ita dai ta san koma waye ne, yana da matsayi babba, tunda mataimakin Darakta da kansa ya damƙa mata wannan aikin.

Yinka kam ta lula cikin nazari. Can ta ce “Ai ko na san wannan sunan, kamar na taɓa karanta hirarsa a wata mujalla ta fasaha. Ina ga ɓangaren ƙere-ƙere yake, ko wani abu makamarcin haka.”

Cikin fara’a suka rabu da Yinka. Ta duƙufa a kan teburinta, domin ta fara nazari. Sai kuma ta tuno kiran Abbu, nan da nan ta bar abinda take yi, ta nemi wayarsa.

Ƙwarai Allah-Allah take Asabar ta yi, ba don komai ba, sai don ta ga wannan mutumin, domin kuwa a ɗan guntun binciken da ta yi, domin haɗa tambayoyin da za tai masa ranar Asabar ɗin. A fahimtarta koma waye ne MASDOOK ABUBAKAR SA’EED. Tabbas ba makawa babban mutum ne, mai kaifin basira, sanin ya kamata da kuma haƙiƙancewa da sadauƙar da kai ga abin da ya sa a gabansa.

Domin yana da shekaru ashirin da biyu a duniya ya kammala karatunsa na digiri na biyu (Master). A ɓangaren aikin Injiniya na ƙera jiragen sama. (Aerospace Engineering). Sannan yana da shekaru ashirin da huɗu ya fara aiki a kamfanin (Airbus) a yankinsu da ke UK, inda ya samu aikin ne a dalilin wani tsohon Farfesansu da ya ke da faɗa a ji a kamfanin, shi ya bada sunansa ta hanyar yabo (Recommendation), aka neme shi, ya kuma lashe gwajin da aka yi masa.

A shekaru ashirin da shida ya kammala karatunsa na bincike, har ya samu takardar shaidar zama Dakta ɗinsa (Doctor of philosophy), inda nan ma ya ƙara ƙwarewa kan aikin kwangila ta ƙera jirage. Daga lokacin ne kuma ya faɗa cikin tawagar wani gagarumin aiki da suka yi na kamfanin (Airbus and Airbus groups).

Wanda ya janyo masa samun ɗimbin nasarori, har ya kai ga ana tunanin a baƙaƙen fata yana cikin manyan fitattu ashirin na wannan fagen. Shekarunsa arba’in a duniya. Ya kai muƙamin manyan kamfani, masu bin diddigin aikin da aka sa a gaba, masu tabbatar da cewa an kammala cikakken aiki akan lokaci.

Da kuma gwajin ayyuka a lokacin da aka kammala su. Yanzu haka ana sa ran yana daga jerin sahun farko a cikin waɗanda za su lashe kwangilar da za a bayar na ƙera sabbin jerin jiragen amfanin yau da kullum, a wannan kamfanin dai na (Airbus).

Ko ba ta gan shi ba, ta san ko ta ina mutumin ya yi, sai dai abin mamaki, baya ga waɗannan fitattun nasarorinsa da duniya ta sani a kansa, ba wani bayani sosai game da wannan bawan Allan, ita dai alfahari da nishaɗi kawai ya sanyata jin kasancewarsa ɗan ƘASARTA ne. A take kuma take jin ta yaya za ta iya fuskantar wannan mutumin da ya zaga duniya, ya yiwo ilimi daban-daban, ya game su wuri guda?

Dole ta duƙufa wajen neman ƙarin bincike, duk da kuwa ta ga furudusoshin shirin sun aika masa samfurin tambayoyin da zai tsammanta daga garesu, a nata ganin ya zamo mata ƙalubale ta iya karawa da mutum mai irin wannan matsayin da iliminsa.

Barcinta ragagge ne a daren Asabar, sai da ta haɗa da addu’a, ko ta samu natsuwa, domin kuwa ba ta isa ta watsawa Mr. Kamaal ƙasa a ido ba, yadda ya amince da ita, ya damƙa mata wannan babban aikin.

Ƙarfe sha ɗaya za ayi hirar, don haka tun tara saura tana wurin aiki, domin a kammala duk wasu shirye-shiryen da suka dace a yi. Tun jiya an nuna mata yadda komai zai gudana, domin haka yanzu abu ɗaya ya yi saura, shi ne baƙonsu na musamman.

“Mihjana za ki iya, kar ki ɗaga wa kanki hankali, ke da ki ka gabatar da shirye-shirye tundaga cikin gida har zuwa waje, mai zai sa ki ji ba za ki iya wannan ba, ki tuna kawai dole ki kula da haɗa ido da baƙon “Eye contact”. Ki ɗauka kawai ku biyu ne ku ke zaune ku ke wannan hirar, ki mance da duniya, baya ga gabatar da shi da za ki masu, ki natsu, shi kenan ba ki da matsala.”

Ajiyar zuciya ta yi, da ta ji bayanin ƙawartata, tana faɗa kamar wani cin biredi da shayi. Amma ga mamakinta, sai ta ji ta ɗan samu natsuwa. Ƙarfe goma da kwata tana cikin (Studio), ta samu labarin baƙonus ma ya iso.

A wannan lokacin Shola na gyara mata kwalliyarta, sanye take cikin jilbaab mai duhun launin bula da kuma hijaab mai hasken bula ɗan madaidaici zuwa saman ƙirjinta, bai cika ado ba, amma ƙwarai kayan suka fito da ita kamar wata ‘yar Turkiyya.

Tana ƙara bin ɗan rubutunda ta yiwo ne a takarda, sai ga shi nan sun shigo da Mr. Kamaal.  Ai ba shiri ta zabura daga mazauninta, cikin zare idanu ta ce “Mr. Abubakar!” Sai kuma nan da nan ta kula da rashin dacewar abin da ta yi, ta yi saurin bada haƙuri, sannan ta gaishe shi cikin murmushi, saboda kar oganta ya fahimci akwai matsala. Shi ya sa ta ce “Na ji daɗin haɗuwa da kai, don na sha jin labarinka”. Kallonta ya yi, ya san daɗin ganinsa, shi ne abu na ƙarshe da yake ran matar.

Amma matsala ɗaya ita ce, sunan wannan shirin, domin kuwa ba ta san ta inda za ta danne abin da take ji na fushi game da wannan mutumin ba, a cikin minti talatin, har ta samu kimtsuwa, ta yi masa tambayoyin da suka dace.

Sanye yake da jacket Suit, kusan shigen kalan kayan jikinta, mazaunin aninai biyu ne, a saman Coat ɗin da ke jikinsa, amma guda ya maƙala. Rigar cikin ruwan toka mai ɗan haske. Bai saka Neck tie ba, sannan aninin rigar cikin na can kusa da wuya a buɗe take.

Har yanzu ba za ka taɓa ce masa Bahaushe ba, sai dai ko Balarabe, saboda yadda fatarsa take sheƙi, bayan hasken ma da yake da shi, ga gashinsa a kwance lub-lub! Yau kam kamar ma ya ƙara fitowa daban. Koda yake don dai yau ɗin ta haɗu da shi kusa-kusa ne.

Sai kuma ta yi tunanin a duka haɗuwarsu, yaushe ne ba su haɗu kusa-kusa ba? Kawai dai mutumin ya iya nuna isa ne. Yau kam ta ga ya saki fuska, ba kamar haɗuwarsu a Tel Aviv ba, ko Frankfurt, ta kasa yarda da cewa satin da ya shuɗe ne kawai mutumin nan ya dagula rayuwarta.

Ba ta kula da lokacin da aka ba shi wurin zama ba, har aka nemi yi masa (Touch up), amma ya nuna baya buƙatar hakan, goge fuskarsa ya yi a tsanake. Yana zaune tamkar ya saba yin wannan hirar, koda yake me take tunani? Dole ya saba mana, ba kamar ita ba da yau ne ranarta ta farko. Baya ga lokacin da suka gabatar da shirin tare da Faiz, amma Mr. Kamaal ya rasa duk duniya wa zai gayyato a wannan ranar, sai wannan…  Wannan Mr. Abubakar ɗin.

Wato dama shi ne Masdook Abubakar ɗin kenan? Dole ya yi mata abin da yake so mana, don yana gadara da matsayinsa a duniya da kuma iliminsa. Anya za ta ma iya masa tambayoyin ba tare da ta yi masa mugun hali ba?

Wata zuciya ce ta ce mata, ‘Dole ki kula, wancan rayuwarki ce, wannan kuma aikin ki ne, dole ki banbance biyun.”  Da ƙyar ta samu hannunta ya daina fitar da zufa, dai-dai lokacin Daraktan shirin ya fara kirga 4, 3, 2, …

*********

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *