A Sackful Of Wishes

Hadiza Musa, 25-years old, has been through hell. As a bubbly, fun loving teenager, she marries the impulsive Abdurrazaq Zanna, known as AR, and for eight years suffers, starvation, rape and mental abuse from an increasingly obsessive husband. The death of her beloved father, followed by the death of her young son from neglect, brings matters to a head. Hadiza determines for a divorce just as AR insists they are meant for each other forever. A battle for survival ensues in which scars come to light and allies come from unexpected places: the prize is a chance at a new life for Hadiza Musa.
A Sackful of Wishes is the first book in The Hadiza Trilogy.

Umm Adiyya

Hannunshi yake kadawa kan sitiyarin motar, yana tafe yana tunanin abubuwa da dama, kwarai ya san cewa ba karamin kuskure yayi ba da ya sake barin Umm Adiyya ta shiga rayuwarsa ko da kuwa ta fuskar aiki ne, duk da kasancewar ba yanda za ayi ya yakice ta daga rayuwarsa saboda abun da ya hadasu ba karamin abu bane da zai warware a dare daya, abun da ya hadasu dangataka ce da ba ta rabewa ba, a tunaninshi ya mance da ita ya sa ta a gefe bazata taba tayar masa da abubuwan da ya zaci ya adanasu ya boyesu a wani lungu a can cikin kirjinsa ba, sai dai yau abun da ya gani a tare da Adiyya sun motsa masa abubuwa da dama masu dadi da masu daci.

Amma ya zama dole ya dubi bangaren dacin yayi aiki da shi saboda hakan zai fi fishe su, daga shi har ita. Har rana mai kaman ta yau bazai taba mance abunda ya faru ba. Birki yaja da karfi a dalilin wata motar da suka kusa yin karo, ashe tsabar tunani ya bar kan hanyarsa ya hau wata daban.

“Zaid Abdurrahman ka wuce haka!” Ya fada a bayyane yayinda ya yanki kwanar Darussalam Close dake Wuse 2 inda shiryayyen gidansa yake.

Zubar Kwalla

Rahaanen Nana, Rahanen Terawa.  Sunan da ake kiranta kenan tun da kuruciyarta sai dai Rahane bata san dadin kuruciya ba kaman ko wani yaro mai shekarunta, saboda yanda mai duka ya aiko mata da jarrabawar rasa mahaifinta a dai-dai wannan gaba. Rashin mahaifi ya janyo mata rashin mahaifa da nisantar mahaifiya inda ta fada rayuwar bauta a gidan yarta Adda Fatu. Ta zaba mata rayuwar kyara, ta hane ta jin dadinsa a lokacin da yaranta suke jin dadin nasu rayuwar ta zamo musu 'yar boyi. Rahaane tayi gamo da masoyi na kwarai wanda take fata zai dauketa daga wannan rayuwar, ga kuma Adda Fatu ta fitar mata da nata zabin sa'an mijinta. Imraan Abdl-Jawaad dan gata, dan kwalisa wanda baya neman abu ya rasa. Gani daya Allah ya hada zuciyarsa da Rahaanen Terawa. Bashi da buri duk duniya illa ya mallaketa a matsayin mata koda ya kama yayi abun da aka dade ana nusasshi yayi ya gagara. Dr. Nasir Salihu, likita mai cin ganiyarsa, dan ajin gabawanda ya rike zumunci da iyalansa sama da komai. Sai dai matsala daya d ake ci masa tuwo a kwarya iyanda mai dakinsa take halin ko oho da amanar dake hannunsu ta 'yar marainiyar 'yar wansa da ya rasu ya bari. Hanya daya ne na samun zaman lafiyarsa da matarsa shine ya kara aure. Kuma ya ga matar da ta dace. Shin Rahane zatayi sa'an kare soyayyarta ko kuwa za a ci galaba a kanta ta fada gidan Dr. Nasir Salihu? Shin ta san shirin Dr. Nasir akan aurenta don tayi raino? Shin Imraan zai bari Rahaane ta subuce masa?

Halin Girma

Masdook Abubakar Sa’id, da na biyu a cikin ’yan gidansu goma sha hudu, sannan mashahurin injiniyan tsara jirgin sama yana fama da wani cakudadden al’amari a rayuwarsa.
Ba abunda yake damunsa da rayuwa, ba kuma abunda ke burgesa da rayuwa bayaga aikinsa da tsohuwar kakarsa. Har sai da ya hadu da Mihjanaa Suraj a filin Jirgi ta karu a jerin matsalolinsa.

Mihjana Suraj Suyudi, macen da tayi fice a fagen aikinta na ‘yar Jarida a shaharerren tasha mai zaman kanta. Ba abunda ta ke so fiye da aikinta da farantawa Abbunta, Uba tamkar dubu. Duk da akwai abunda Abbunta ya nema a wurinta da yayi mata tsauri har ta juya masa baya taki bashi wannan. Hakan bai sa kima ko kuma soyayyar mahaifin nata ya ragu ko kankani a zuciyarta ba.

Amma haduwarta da Masdook a filin jirgi sanadiyyar rasa jirginta da tayi ya sa ta kara fuskantar bukatar mahaifinta mai tsauri.
Shin MIhjana zata iya nuna Halin Girma ta ida wannan nufin? Ko kuwa Masdook da Abbunta zasuyi nasara akanta?